Tinubu Ya Nada Majalisar Gudanarwa Ta Aikin Hajji, Fitaccen Malamin Sakkwato Ya Shiga Ciki

 Tinubu Ya Nada Majalisar Gudanarwa Ta Aikin Hajji, Fitaccen Malamin Sakkwato Ya Shiga Ciki

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabuwar majalisar gudanarwa ta hukumar jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON).

Majalisar dattawan Najeriya ce za ta tabbatar da sabbin nade-naden. 
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ajuri Ngelale, kakakin shugaban kasa ya saki a yammacin ranar Laraba, 10 ga watan Janairu. 
Sanarwar ta ce Tinubu ya nada mutanen ne a cikin "kudurinsa na tabbatar da aikin Hajjin 2024 ya tafi daidai ba tare da matsala ba." Ga jerin mutanen da aka nada a hukumar aikinb hajjin: Jalal Arabi — Shugaba (a ofis)
Prince Anofi Elegushi — Kwamishinan ayyuka
Aliu Abdulrazaq — Kwamishinan manufofi, ma'aikata da kudi
Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal — Kwamishinan tsare-tsare da bincike.
Wakilan yankin
Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya
Abba Jato Kala — Arewa maso Gabas
Zainab Musa — Kudu maso Kudu
Farfesa Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam
Sheikh Muhammad Bin Othman — Arewa maso Yamma
Tajudeen Oladejo Abefe — Kudu maso Yamma
Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas
Farfesa Adedimeji Mahfouz Adebola — Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya.