Tinubu ga gwamnoni: Ku ajiye bambancin siyasa ku fuskanci al'umma 

Tinubu ga gwamnoni: Ku ajiye bambancin siyasa ku fuskanci al'umma 
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su ajiye bambancin siyasa a gefe su hada kai da gwamnatin tarayya wajen gina kasa.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a lokacin bude-bakin azumin watan Ramadan tare da gwamnoni a fadar gwamnati da ke Abuja, a jiya Alhamis.
Ya kuma jaddada muhimmancin ajiye siyasa a fuskanci mulki, inda ya ce akwai bukatar hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki.
“Tunda mun fahimci bukatar gina al’ummarmu tare, lokacin siyasa ya wuce. Yanzu lokaci yayi na mulki.
“Mu ‘yan uwa daya ne kuma iyayenmu daya; mu na zaune a gida daya, amma a dakuna daban-daban mu ke kwanciya. Dole ne mu hada kai da yada soyayya a tsakanin juna,” inji shi