TAWA RAYUWAR
By Maryama
Page 2
the beginning💔
Da kyar muka samu abin hawa dake har an fara kiran magriba, adaidai kofar gidanmu aka ajje mu normal irin ginine na talakawa amma masu rufin asiri kofar gidan mu koface sai gefe wani dan shago karami inda baban mu kafin ya rasu yake zama, yanzu kuwa babu komai cikinsa aminatu ce ta kama ni dukda itama tana ji da nata al’amarin amma ni nafita shiga wani hali dan shigata cikin su amra tamkar nakai wa kura fida ne gefe daya ga mommy allah kadai yasan irin cakwakiyar da za’a yi, da sallama muka shiga saidai tun a soro nake jin kukan mahaifiyar tamu cikin tsananin firgici da gigicewa muka ruga izuwa ciki…
Farar dattijuwa ce wadda a shekaru bazata gaza 40
ba amma kamar wadda tayi 50 saboda yanayin tsufa daya fara bayya mata, kuka takeyi cikin halin rashin sanin abinyi saman cinyarta budurwa ce yar shekara 20 kakkafe kamar mai figar ruwa idanunta sun juye da alama bata cikin haiyacinta gefensu ma budurwa ce wadda tadanfi marar lafiya a girma itama kukan take, a wannan halin NAJMAH da aminatu suka iske su aunty wadda take mahaifiya garesu, da gudu najmah ta kama anisa tana jijjaga ta amma inaa bama tasan sunayi ba “ aunty mu kama ta ko gidan baba doctor ne mu kaita nasan yana gida yanxu “ amina tayi maganar tana matsan kwalla da tausayin kansu da kuma yar uwarsu wadda tunda aka haifeta take tare da wannan lalurar lokaci zuwa lokaci idan ciwonta ya tashi tamkar bazata rayu ba kuma sunje asibiti amma har sun gaji ga kuma karamin karfi danma kawu hafiz da kawu aliyu suna matukar taimakawa saidai yau da gobe sai allah amma har yanxu babu wani sauki tare da ciwon nata, da kyar amina tayi ta lallashe su suka riko ta najmah ta kama hannunta itama amina ta kama gefen daya ita kuma mahaifiyar tasu ta saka mata hijab dukda itama ba lafiya gareta ba tana fama da ciwon zuciya ne shiyasa ba’ason yawon tashin hankalin ta amma dole take dannewa dan su tasu kaddarar kenan, islam ce ta riko hannun auntyn tasu da take kokarin bin bayansu tana kuka abin tausayi, “kiyi hakuri mu jira su dawo nasan in shaa Allah komai zai zama tarihi a rayuwar mu aunty, zamuyi farinciki kamar yadda kowa yakeyi anisa ma zata tashi kamar kowa mudai mu cigaba da mata addua” kalaman islam ne suka dakatar da aunty daga kokarin da takeyi nason bin bayansu dan ganin halin da yar ta take ciki wasu hawaye masu tsananin zafi suka sulalo kumatunta saidai duk halin da take ciki ba karamin godiya take da allah ya azurta ta da ya’ya na gari gasu da hankali iya lafazi kuma a koyaushe burinsu kada tayi kuka burinsu su kwantar mata da hankali, murmushi mai ciwo ya subuce mata a sannu takai hannu jikin kirjinta jin yadda zuciyarta yake bugawa da karfi kamar zai faso kirjinta ta fito a hankali ta sulale a wajen saijin karar faduwar kawai islam dake duke taji wani kara ta fasa tayi kan auntyn tasu wadda suke jinta itace duniyarsu.
Bayan fitarsu direct neighbor dinsu suka shiga gidan doctor ne kuma yana matukar taimaka musu duk lalurar data same su shi yake tsaye har sai yaga da sauki cikin ikon allah, daga farkon shiga cikin gidan parlonsa yake da sallama suka shiga dawowarsa kenan daga masallaci yaji sallamansu iso yayi musu kafin suka shiga har sannan anisa a kame take sai idanunta dake bude gasu masha allah da girma anan carpet suka shimfideta shi kuma ya sauko daga kujera bayan sun gaisa yake tambayarsu ciwonne ya tashi eh suka amsa masa a hankali ya dafe goshinsa , dattijo ne amma ba cen ba yana da mata daya da ya’ya ukku sosai suka daukeshi yayansu dan idan lalurar su ta tashi kafin su kawu su kawo musu dauki shi zai fara, first aid box ya dauko acen kuryar dakinsa kafin ya dauko wata allura da idan ciwonta ya tashi yake mata nan ya hada da sauri kafin ya mata ita su najmah duk sunyi cirko cirko kana kallonsu basai an gayamaka irin tashin hankalin da suke fuskanta ba tun suna kananun yara har kawo girmansu, wani huci mai zafi na sauke mun fi minti 10 kafin mukaji anisa taja numfashi mai karfi ta sauke a sannu idanuwanta suka rufe bacci ya kwasheta na wahala sai a sannan muka ajje ajiyar zuciya murmushi ya kubuce mana harda shi doctor kafin ya kallemu yace “Alhamdu lillah yanxu saiku barta anan zuwa bayan isha sai maryam ta rako ta (diyarsa kenan best friend din najmah) da to muka amsa kafin mukayi masa godiya dukda munsan bayaso amma ya zama wajibi a garemu, batare damun shiga ciki ba muka fito daga gidan inajin sanda yake kwalawa matarsa kira wadda muke kiranta da umma.
Shigarmu gida wani tashin hankalin muka riska islam duke a wajen aunty tana mata fifita ga hawaye yana zuba a idanun auntyn mu gashi tanajin a jikinta ciwon tane ya tashi amma bata son ta kara tada hankalin mu, jiki a sabule muka zauna muka sata a tsakiya saidai ta kalli wannan ta kalli waccen gaba dayanmu mun kasa magana , cen ta budi baki da kyar tace “ kuje kuyi sallah “ dafe goshi nayi dan wallahi shaf na manta ko sallah bamuyi ba ta magrib harga isha tana kawo wa da sauri muka fara rige rige nida su islam bayan munyi ne nutsuwa tazo mana kafin aunty tace “ya jikin anisa “ aminatu ce ta amsa mata da sauki kafin tace bacci take sai doctor yace a barta maryam zata rako ta idan ta tashi daga nan ba wanda ya sake magana har lokaci mai tsayi kafin a bazata aunty ta jefo mana maganar da yasa muka fara ido ido nida amina sai yanxu ma muka tuna halin da muke ciki na aurar damu da kaka yake kokarin yi ga yan uwanmu.
Matar kawu hafiz mommy kenan itace ta fara riskar maganar hadin auren da za’awa danta wanda ta dauki son duniya ta aza masa wani irin lailayo ashar tayi ta sauke wa amira da amra da suke bata labarin kafin tace “ ai kuwa lokaci yayi da zan nunawa nusaiba (aunty) gaba daya rayuwarta a tafn hannuna take dan da’in hada zuri’a da ita gara in hada da karuwa mai zaman kanta wallahi bata isa ba duk wani asiri da tayi saidai ya koma mata amma badai zai kare akan dana ba “ ta kare maganar tana huci duk idanunta sunyi ja saboda tsananin bakinciki da tsanar nusaiba da yake dawainiya da ita (Niko nace ko menene sila?) “ mommy kada ki yadda haka nan sun gama tambadewa a titi yanxu kuma a makalawa danki ita bayan a idanun ki dai babu wani saurayi daya taba maganar zai aurensu saboda bakin jinin da suke dashi ga rashin mashinshini “ amra ta fadi tana tabe maki zuciyar ta fal hassada saboda kaf familyn su ba’a taba haihuwar kyawawa ba kamar yayan aunty more especially ma najmah duk ta fisu kyau na asalin buzaye dan auntyn su buzuwa ce daga niger babansu ya auro ta kuma duk yayan kamr ta sukeyi aminatu ce ma tayi kama da baban nasu dan ta dauko kiba amma ba mai muni ba kuma tayi dan duhun fatar sa, Amira ce tayi kwafa tace “ni kuwa idan akayi auren nan wallahi saita yi dana sanin shigowa cikinmu “ buge mata baki mommy tayi kafin tace “ a gidan uwarki za’ayi auren? Shegiya mai mugun baki “ turo baki gaba tayi tana bata fuska jin zafin ya ratsata har kwalwa, abida da take zaune ce ta dago ta kallesu kafin tayi murmushi tace “ ku kwantar da hankalin su dan kuwa idan akwai abinda Yaya farouk ya tsana to wannan shegiyar ce najmah, dakatawa tayi da magana tana murmushi dan duk ciki ta fisu wayo da mugunta ta karkashin kasa dukda kuwa itace karama kafin taci gaba Da cewa” har abada banajin zai sota kuwa dan tsakanin su babu jituwa tamkar haduwar rana da wata “ lumfa sawa tayi kamin tace “so you guys sai ku sanyaya zuciyarku bayan gaba da kiyayya babu komai kuma koshi bai dauki mataki a kanta ba mu zamu dauka wannan alkawari nane su da jin dadi har abada “ kwashewa da dariya sukayi gaba daya kafin mommyn tace “ hmm dukda haka nidai bazan bari yayi auren ba saboda babu lafiyayyen namijin da zaiga najmah a gidansa yace baiso taba “ daga nan suka cigaba da hada yadda zasuyi su hana auren kuma su musgunawa aunty da ya’yanta, bayan sun gama ne mommy ta tashi ta nufi dakinta ta dauki wayarta dake saman mirror kafin ta danna kiran wata number da akayi saving da mujahida bayan ringing uku aka daga nan take labartawa matar abinda ake ciki akan danta farouk da yar makiyar ta wato najma itama daga cen bangaren banda zagi da cin mutumci bata komai harda cewar har kotu ko human rights sai sunkai tsohon banzan dayakeso yayi hadin auren nan (wato kaka😂) ta inda ta shiga bata nan take fita ba ganin za’ayiwa yarta salhohuwa bayan bata ma fara cika burinta ba.(🤔) har tafi mommy zagewa daga nan dai suka gama kulla kitumurmurar da zasu aiwatar kafin sukayi sallama, mommy ta ajje wayar tana yin kwafa ganin tun ba’aje ko ina ba abubuwa zasu cabe musu bayan ita ko murmushi bakinciki takeyi idan nusaiba ko ya’yanta sukayi itace bata tashi daga gun ba
Harsaida abba(kawu hafiz) yayi kiranta kafin ta nufi dakin nasa nata ta shan magani gefe daya ga zugar da yar uwarta ta gama mata yanxu, a haka ta tura kofar da sallama ta shiga yana zaune a gefen gado yana latsa waya, abba ba dogo bane irin mazan nan ne tsaka tsaki yana da jiki kadan kuma yana da hasken fata gashi mutum ne mai fara’a ga kowa Da son mutane , dagowa yayi ya mata kallo daya ya dauke kai nan ta zauna ta fara huci tana magana da fada akan hukuncin da kaka ya yanke itafa sam abin bai mata ba kuma tana da wadda zata ba farouk gara ma su sake zama dan bazata yadda a dannewa danta hakki ba baice komai ba harta karasa maganar ta kafin yace “kina nufin magana biyu zan saka baba yayi? “ ya jefa mata tambaya take ta diriri ce dan duk iskancin mutum yasan waye kaka inya fada baya canji nan fa tahau kame kame ganin dai ta kasa bashi amsa yasa ya saki murmushin dashi kadai ya barwa kansa sani sai mahaliccinsa kafin ya kama hannayenta yace “calm down zulfa wai meyasa kike tsaurara abune maganar hadin auren nan baba ya riga ya yanke dan haka inma kinada wani abu a zuciyarki game da haka gara tun wuri ki janye dan aure babu fashi in shaa Allah kuma ka da ki manta najmah fa yar uwar Farouk ce sannan bamu san abinda allah ya boye ba kinga gara kada kiyi shisshigi ki barwa Allah komai” yana gama fadin haka ya saketa ya mike a hankali ta bishi da kallo harya shige toilet ya barta tana tunanin menene a zuciyar mijin nata dan wani lokacin yana bata mamaki idan yana wani abun (kamar yaya fa?)
“Me aka tattauna a gurin meeting din? “ zuru zuru mukayi nida amina rasa wanda zai fada mata akayi har tsawon minti biyu islam ce ta kalleni tace “aunty fa tana tambayar ku “ nan ma shiru ne sai hawayen da nake kokarin gogewa dukda a duhu ne amma akwai hasken farin wata hakan yasa aunty ta lura dani kafin ta juya gurin amina da itama hawayen ta shafe, babban dalilin kin gaya mata da mukayi munsan ciwon tane ya tashi koda bata fada ba gashi kuma bamusan wani hali zata shiga ba akan lamarin tunda komai a bude yake, mudin yan uwane amma kuma duniyar mu ta banbanta kuma kowa ya sani “ shikenan zan kira wanda na isa dasu sai su fadamin abinda aka tattauna “ jin abinda aunty ta fada yasa na fashe da kuka ina toshe bakina kafin da kyar na saddakas nace “aunty wai auren hadi za’a mana amina da yaya hassan ni kuma da yaya …” kasa fada nayi wani kukan yana kwace min na tausayin kaina , tunda na fara magana aunty take fadin Hasbunallahu wa ni’imal wakeel a zuciyar ta harna kai karshen magana ta saidai rashin fadin mahadin nawa yasa da kyar cikin karamar murya kamar mai tsoron a jita tace “ keda wa? “ amina ce tayi jan halin cewa “ itada yaya farouk “ sosai muka ga aunty ta zabura ta mike zaune hakan ya kara tada hankalin mu fiye da ko yaushe dan munyi tunanin sai hankalinta yafi tashi akan auren hassan da amina amma sai naga ba haka ba cikin sarewa islam tace “ aunty ko akwai matsala “ sai sannan ta lura da abinda tayi dan haka tayi kokarin ganin tayi calm down kafin tace “ babu komai allah ya sanya alkairi “ sosai kalaman ta suka bamu mamaki har saida na kasa hakuri nace “ kina nufin kin yadda a aurar damu ga makiyan mu aunty?” Girgiza kai tayi hawaye nabin kumatunta tace “ babu abinda zai faru da rayuwar ku sai Alkhairi ina mai horar ku da hakuri komai zai faru gareku ku sani allah shine yake yi kuma duk abinda ya tsara babu makawa saiya faru saidai amsar kaddarar mu yana kara mana kusanci da allah madaukakin sarki kuma duk abinda iyayen naku zasu yanke akanku bazan iya hanawa ba saboda karfin ikon da suke dashi “ta karasa maganar cikin sanyin jiki dana zuciya saidai ita kadai tasan mi take ji tamkar zuciyarta zata fado kasa tsabar ciwo, daga haka mukaga ta mike ta shige daki nan islam tayi ta tayamu jajantawa amma itama a tsorace take kada ace za’a hada ta da wani cikin yan uwan namu dan dama ba’afi wata daya ba kawu aliyu yazo yace mu fitar da maza su aurar damu tunda shekarun mu sunkai amma rashin tsayayyun samari yasa muka kasa har su kuma suka dauki wannan matakin muna nan zaune mun kusa ko minti 20 saiga aunty ta fito da hijab tayi kofar gida a hankali kamar mai rada tace “ ina zuwa kada wanda ta fita cikin ku “ daga haka bata bamu damar tambayar taba dukda munason tambayar, gashi batajin dadin jikinta amma haka muka saka ido harta fice, ina mamakin halin nan na mahaifiyar mu wani lokacin haka zata tashi ta fita batare da munsan ina take zuwa ba kokuma me takeyi ba kuma tun muna tambaya har mun gaji dan kullum amsar daya ce “ naje nasha iska ne ina bukatar keben cewa “ wannan shine amsar ta koda yaushe kuma bamu taba bin bayan taba dan mun yadda da auntyn mu bataza aikata abu marar kyau ba.






