TAWA RAYUWAR
By maryama
villains
family
drama
heartbroke
injustice
Bismillahir rahmanir rahim🤍
Littafin tawa rayuwar 60% true life story ne wanda yarinyar cikin ta bani shi, amma akwai wurare da dama da na kara yadda labarin zai qayatar ya kuma bada darasi ga masu karatu.
1
A duk lokacin da naji ana fadin komai me wucewa ne saidai inyi murmushi a raina badan na yadda cewar kaddarar dake tare dani wani lokaci zata wuce ba…Hakika kowani bawa baya wuce tasa kaddarar don kuwa tamkar rigar jikin mu haka take koda ka cire ta dole zaka nemi wata ka saka, don bazakayi yawo tsirara ba. Saidai kuma a lokacin da farin ciki yazo min a sannan ne na tabbatar da maganar cewa komai mai wucewa ne ,kada kuyi tsammanin rayuwata tamkar ta kowa take! Ni tawa ta banbanta dan kuwa ba kowani bawa bane zai iya jurar daukar kaddarar tawa , ina fatan zaku ci gaba da bin labari na mai ban al’ajabi tare da tausayi, cin amana, kunci da damuwa , zafin kai,soyayya mai tsafta da shiga rai…..
Babban parlor ne wanda ya kasance ba’a budesa a gidan kawun namu indai ba irin wannan ranar ba wadda muke family meeting a ciki ba, cike yake da dangin mu na bangaren mahaifina kowa ka gani dauke yake da matsananciyar damuwa dan kuwa babu wani mai farinciki a cikin mu idan ka dauke kakan mu da kawun nan mu, a kalla zamu kai hamsin da wani abu dan idan ka hademu muda iyayen mu bamu da wani yawa ,set din kujeru biyu ne a ciki da ash masu duhu da kuma brown kirar royal chairs wanda suka kawata parlon matuka babbar kujeran 3 seater kakan mune a kai wanda zai doshi a kalla shekaru 80 da wani abu sauran kujerun kuwa yayyan mahaifina ne da kanninsa a kai sai mu damuke yanmata da matan aure da yan samari da dai sauransu muna saman wani carpet lallausa kalar golden wanda ya kara bayyana kyawun dakin taron. ,kawu hafiz shine babban da a gurin kakan namu sai mabiyin sa kawu ishaq sannan kawu aliyu, kawu nassar sannan babana Al’amin sai autarsu mama rakiya.
Kawu hafiz ne bayan yaja dogon numfashi ya kalli wata yar budurwa dake gefen kujera tana ta sharar hawaye tana shassheka cikin kwantar da murya da lallashi yace “Aminatu kukan nan ya isa ya kamata kiyi hakuri hakan nan kinsan bazamu cutar dake ba a matsayin mu na iyayenki kuma ai Hassan dan uwankine dan haka banason in kara ganin kukanki kinji ina fatan zaku amshi wannan hadin da hannu biyu, kunga zumuncin mu zai kara karfafa koba haka ba? “ ya kare maganar da tambaya shima kawu ishaq ya karbe zancen da cewa “tabbas hakan yayi dan nasan hassan bazaka bani kunya ba aminatu bata da matsala kuma yar uwar kace dan haka ku rungumi juna in shaa Allah muma zamu taya ku addua tare da fatan zaman lafiya mai dorewa “
Hassan da har yanxu kansa yake duke a hankali ya dago ya dora idanunsa akan yarinyar da ake ikirarin an bashi bata da laifi black beauty ce yar duma duma saidai shi a saninsa ko kadan babu jituwa tsakanin ya’yan umman sa da ya’yan auntyn tashi dukda baisan menene mafarin abin ba , shi idan ta tashi za’abi baya da matsala da auren tunda duk wanda yasan ya’yan aunty ansan suna da tarbiyya tsantsa ga girmama na gaba amma idan ya tuna umma sai yaji auren yana neman fita a ransa, bangaren Aminatu kuwa sanin tsananin kiyayyar dake tsakanin dangin biyun yasa take jin da tana da iko da ta hana wannan auren itama a nata bangaren yaya hassan baida matsala amma yaya zatayi da yan uwansa? Mahaifiyar sa da duk wanda ya dangance su? Tuno Hakan yasa ta take zubarda hawaye batare da tayi kokarin tsaida su ba saidai dukda tashin hankalin da suke ciki saida sukaji ya karu sanadin maganar da tsoho mai ran karfe ya fadi “ hassan da aminatu mun gama da maganar ku yanxu ta NAJMAH da FAROUK zamu dasa dan so nake bikin naku duka kada ya wuce wata 2 in shaa Allah masu zuwa“ a zabure mafi yawan mutanen parlorn suka dago, a take naji tamkar a datsa min guduma a kai cikin gigicewa har bansan lokacin da bakina ya furta “KAKA dan girman Allah kada kace haka wallahi babu wata soyayya dake tsakanina da yaya farouk saidai tsantsan tsana dan allah kad…” dukan da mama atika ta kaimun ne ya sanyani kasa karasa maganar tawa take na fashe da kuka mai matukar ciwo bawai ina kukan dukan bane a’a ina kukane saboda wulakancin da yaya farouk yake mana dagashi har yan gidansu sam babu jituwa tsakaninmu ga tsantsar tsana da mahaifiyarsa mummy tayi mana wanda hakan ya kara sa muka janye jikinmu daga familyn mu tamkar bamu da kowa dukda a cikinsu akwai wanda suke janmu a jiki, , hakika banajin zan iya amincewa ayi hadin auren mu dan kuwa mudin mun banbanta shidin hagu ne ni kuma dama ce, cikin kuka na daga murya nace “dan allah kaka ka taimaka ni wallahi bana sonshi nayi maka alkawarin zan fiddo mijin aure amma dan allah kada ku hadani da yaya farouk” mama rakiya ce ta kara kawo hannu zata mazgeni kaka ya daga mata hannu yana fadin “ ya isa rakiya “ kafin yayi murmushi ganin duk wanda ya kalleni yasan bana cikin hayyacin na daga ni har aminatu da hassan dama shi yaya farouk bai samu damar zuwa taron ba dan haka baisan wainar da ake toyawa ba, a hankali wani kukan ya kara kubuce mun duk tausayin amina da nake sai naji ashe nice abar a tausaya wa dan kuwa yaya hassan bashi da wata matsala idan ka dauke ta yan gidansu shi kuwa yaya farouk shi kansa matsala ne balle aje ga mommyn shi ga kuma sisters dinsu , bansan me muka tsare musu ba daga ni har auntyn mu da duk yan gidan mu ma dan ko kadan bamu da farin jini agun dangin mu ko kuwa dan mu marayu ne shiyasa? Bayan hakan munfi kowa karamin karfi dan abban mu kafin ya rasu shagone garesa na provision kuma ba wani babba ba.
A cikin nutsuwa kaka ya ci gaba da mana nasiha tare da nuna mana ingancin auren gida kuma ya kara jaddada mana babu fashi sannan zai sami farouk din shima ya fada masa dan kuwa bayason abin ya dauki lokaci mai tsayi sannan kuma batun karatun mu bayan aure idan mazajen mu sunaso sai mu cigaba da yi daga nan aka tsaida 2 months in shaa Allah masu zuwa sai ayi biki yana kare jawabin sa kawu hafiz ya rufe taro da addua dake shine babba a cikin ya’yan kaka. Jiki a sabule yan uwanmu suka ringa fita wasu suna tausayin mu kamar ya’yan kawu nassar sauran kuwa banda harara da kwafa basa komai burinsu bai wuce a tashi su tafi gida ba dan kaiwa iyayen su gulma, Amina ce ta matso kusa dani fuskar ta shabe shabe da hawaye saidai babu yanda zamuyi kaka magana daya yakeyi baya biyu kuma munsan tunda ya furta wallahi sai anyi saidai mu mutu ko kuma wani iko na allah, maganar mama rakiya tasa na dago fuskata “ wato ke tatatta marar ta ido ana magana kina maidawa manya ko? To wallahi saidai ki bunne kanki daga ke har uwar taku mai neman ta rabamu daku saboda taga an barku a gunta wato ita isasshiya kum…” “ rakiya magana ta wuce fa ku kuma ku tashi ku wuce gida kafin dare yayi “ kawu aliyu yayi maganar yana kaiwa kofa shima, a hankali amina ta kamani har lokacin ban daina zubda hawaye ba muka fita batare da mun kalli kowa ba dake harabar gidan na kawu hafiz ba muka nufi get duk wanda ya kalle mu yasan muna wani hali more especially ni da bansan ya zan kare da yaya farouk ba gara ita aminatu da sauki ,hannu biyu nasa na dafe kaina dake barazanar rabewa biyu ga hajijiya dake neman kada ni, aminatu ce ta kalleni da idanunta luhu luhu tace “ najmah ki daure dan allah mu samu abin hawa kinga magriba tana karatowa ga halin da mukabar anisa kuma kinsan aunty ma ba lafiya gareta ba please ki daure “ gyada mata kai nayi ina cije lebe na na kasa sannu a hankali har na mike daga kan dakali (dabe) dake kofar gidan neighbor din kawun namu.
Sunana FADIMATU AMIN saidai ana kira na da najmah shekara ta 24 a duniya ya’yan mahaifiyar mu hudu Aminatu ce babba shekara biyu tsakanin mu sai ni sai islam da auta anisa duk baya wuce tazarar shekara biyu, mahaifin mu ya dade da rasuwa dan tun anisa tana yarinya yayi accident ya rasu.
Kaka asalin sunan sa Muhammad ishaq dan asalin kano ne anan yayi aure har allah ya azurta shi da yaya duk maza sai guda daya mace wato mama rakiya, na farkon su shine hafiz, isahq, aliyu ,nassar ,amin, da rakiya kuma kowanne yana da zuri’a kuma kowa anan kano yake da zama kuma a unguwa daya saidai mune kawai gidanmu yadanyi nisa da sauran, familyn mu suna da tsauri sosai kuma idan sukayi magana ta zauna kenan.
Yaya farouk dan kawu hafiz ne dama duk cikin ya’yan kaka babu mai kudinsa, ilimi, wayewa, da sauransu daga shi sai al’amin, amira, amra, abida duk ya’yan mommy ne, kuma duk allah bai hada jinin su damu ba dan idan baka sanmu ba bazakace yan uwa bane idan muka hadu saidai mazan bawai kiyayya suke gwada mana ba badai su shiga harkar mu kuma duk hudubar mommy ce saboda qin da take mana, kawu aliyu ma yayan sa hudu, ukku mata daya namiji Hassan, usaina, hanifa, hamida sai kawu ishaq shima ya’yansa ukku,abban mu yana da mu sai kuma kawu nassar mai ya’ya shidda hudu mata biyu maza sai mama rakiya ya’yanta biyu maza ukku mata itama anan kano take aure (duk a sannu zaku san yan uwan namu da halayan su) wannan shine takaitaccen tarihin mu a gajarce.
A hankali muke tafiya dagani har amina kowanne akwai abinda yake cimai zuciya bamu ankare ba naji an janyomin hijabi nayi baya kamar zan fadi allah ya taimake ni amina tayi saurin rikeni tana kallon Amra da abida sai hanifa da hamida ko waccensu tana jifarmu da mugun kallo tamkar zasu daba mana wuka su kashemu su huta, kara daidaita tsayuwa ta nayi idanuna da suka kumbura saboda kuka na kallesu dashi na budi baki inyi magana amra da take babba a cikinsu tace min “ki rubuta ki ajje matukar kika auri yayana wallahi saina tabbbatar da rayuwar ki ta lalace dan kuwa sai mun hadu mun azabtar da rayuwar ki bake kadai ba hadda ta wannan sakaran “ ta kare maganar tana nuna amina wadda magana ma ta kasa yi musu sai binsu da ido takeyi kamar yadda nima nayi shiru ina sauraren yaya amra “matsiyata masu bakin jini “ hanifa ta amshe zance, murmushi nayi wanda iya kacinsa lebe dan inda sabo mun saba da cin mutumcin yan uwan namu da basa mana kallon mutane nace “ai bani zaku tara ku fadawa ba sai kuje wajen iyayen ku da suka hada auren ku sanar musu ku….” Marin da hamida ta kaimun yasa na kasa ci gaba da maganar cikin zafin rai na kalleta da jajayen idanuna yarinyar da a haihuwa na girmeta amma shine ta iya daga hannu ta kaimun mari haka , saidai maimakon na rama saina tsinci kaina da mata murmushi nace”bashi kika dauka ko baki biyani ba tabbas wani zai amsarmin batare dana kara cewa komai ba na kama hannun amina dake kukan marin da sukamin na jata muka wuce, cikin daga murya abida tace “as as a kara gaba masu bakin hali ya’yan mace “ a tare suka tuntsure da dariya suna tafawa tare da ci gaba da fada mana maganganu marasa dadin ji wanda suka shafe mu da mahaifiyar mu saidai ko kadan bamu juyoba burinmu bai wuce mu bar layin gaba daya ba dan yanxu ba tsanar ya’yan kawu nan mu kadai nakeji ba harda ta kakanmu ma daya hada auren mu dasu.
-minene mahadin kiyayyar su Amina da danginsu?






