Tasirin Da Ke Cikin  Mamayar Da Gwamnan Sokoto Yayiwa  Masu Zuwa Aiki  a Makare

Tasirin Da Ke Cikin  Mamayar Da Gwamnan Sokoto Yayiwa  Masu Zuwa Aiki  a Makare

 

Gwamna Ahmed Aliyu ya yi abin da ya ba da mutane da-dama mamaki a ranar Alhamis, inda ya kuma yi nasarar cafke masu saba doka. 

Daily Trust ta ce Ahmed Aliyu ya dauki mota, ya tuka kan shi da kan shi zuwa gidan gwamnati, a nan ya iske mafi yawan ma’aikata duk ba su iso ba.
A lokacin da Mai girma Gwamnan ya iso ofishinsa kimanin karfe 8:30 na safe ne amma ya samu jami’an gwamnati da-dama ba su ofis a lokacin ciki har da Sakataren Gwamnati. 
Da Gwamnan na jihar Sokoto ya shiga gidan gwamnati, bai samu kowa ba sai masu goge-goge da wata ma’aikaciyar jinya a asibitin fadar gwamnan. 
Gwamna Aliyu ya bada umarni cewa jami'an tsaro  su rufe kofar shiga kuma ka da su kyale wani ma’aikaci ya shigo ciki a dalilin makarar da suka yi. 
Rahoton ya nuna haka dai aka bar kofar a garkame har zuwa kusan karfe 1:00 na rana. 
A cikin jerin makararrun aka bari a waje har da manyan jami’an gwamnatin jihar Sokoto da kuma hadimai da mukarraban Gwamna da aka mamaya. 
Da yake bayanin abin da ya jawo ya hana ma’aikatan shiga ofis, Gwamna Aliyu ya nuna bai dace a rika wasa da abin da ya shafi aikin gwamnati ba. 
"Wannan ba abin wasa ba ne. Abin da ake bukata daga duk wata gwamnati da take yi da gaske shi ne a rika biyan ma’aikata albashinsu a kan kari. 
"A lokacin da na zo, na biya albashin watanni biyu a cikin makonni uku. 
"Shiyasa na tuko kai na zuwa ofis domin direbobi ba  su zo da wuri ba. 
"Yanzu ba zan fada maku matakin  da zan dauka  nan gaba ba domin kuma a makare ku ka zo (yana nufin ‘yan jarida)".