Home Uncategorized Tambuwal@60:Gwamnan Sokoto ya ki karba gayyata

Tambuwal@60:Gwamnan Sokoto ya ki karba gayyata

7
0

Tsohon Gwamnan Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya cika shekara 60 a duniya in da ya shirya wani taro domin murnar zagayowar ranar.

Manyan mutane jagorori a Nijeriya sun halarci taron kamar tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da shugaban majalisar dattijai David Mark da tsohon kakakin majalisar wakilai tsohon gwamnan Katsina Aminu Masari da wasu tsaffin gwamnoni da Sanatoci da manyan ‘yan siyasa.

Gwamnan Sokoto Dakta Ahmad Aliyu bai halarci bukin ba, duk ware masa wurin zama da aka yi kuma bai tura wakilci ba, abin da ya haifar da cece ku ce a tsakanin magoya bayan jagororin guda biyu.

Magoya bayan Sanata Tambuwal suna ganin rashin kyautawa ce Gwamnan ya yi, ganin mai bukin ya gayyyace shi tare da ware masa wuri mai daraja amma ya ki sanyawa bukin albarka, duk da siyasa ba gaba ba ce.

Magoya bayan Gwamna Ahmad suna ganin abin da ya yi, ya dace domin taron da aka yi na siyasa ne an labe da bukin ne wanda shi ya fahimci hakan ya sa bai je ba domin suna da bambancin jam’iya.

A kafofin sada zumunta na zamani da wuraren zaman mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu kan dacewa ko rashinta ga halartar taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here