Tambuwal@57: Mataimakin Gwamna  Da Mukaramban Gwamnati Sun Kunya Ta Shi

Mataimakin gwamna da Sakataren gwamnati da shugaban ma'aikatan jiha dana fadar gwamnati, ba su sanya taya murna a jaridu ba. Kwamishinoni 31, daya ne kawai kwamishinan lafiya ya sanya a jaridar daily trust da Leadership. Shugaban jami'a mallakar jiha da makarantar kimiya da fasaha ta Ummaru Ali Shinkafi da kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari suma ba  labarin sanya taya murna ga gwamnan ba ba za ka ce dai ba su san  muhimmancin hakan ba, don jagororin shaihunnan malamai ne.

Tambuwal@57: Mataimakin Gwamna  Da Mukaramban Gwamnati Sun Kunya Ta Shi

 

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a  wannan Talata 10 ga watan Junairun 2023  ya cika shekara 57 da haihuwa rana mai muhimmanci gare shi da iyalansa da duk wani masoyinsa.

Gwamna Tambuwal wannan lokacin yana buƙatar sadaukarwa da bayyana cewa shi jagora ne da ya amfanar da duk wani makusancinsa musamman wanda yake riƙe da abin hannunsa a cikin gwamnati yake ko shi ɗan siyasa ne ko ɗan kasuwa.
A yanda abubuwa ke tafiya  Tambuwal ya tsaya takarar sanata  a 2023 wannan ne ya jawo hankalin Managarciya ga bibiyar manyan jaridun Nijeriya da Tambuwal ke murnar zagayowar shekarar haihuwarsa domin ganin irin cire shi kunya da nuna sadaukarwar da mukarabansa za su yi wanda hakan tura saƙo ne ga duk wani mai son yin jayayya da Tambuwal ya sani cewa jagoransu yana da masu kashe masa kunya da shirin sadaukarwa gare shi ko bayan ya sauka mulki domin wannan ce shekara ta karshe a saman kujerar gwamna.

Kash! Sai dai hakan ba ta samu ba domin sun nuna abin da suka samu ƙarƙashinsa nasu ne da iyalansu, shi ko da yake neman rike gidan siyasarsa  ya nemawa kansa masu sadukarwa irin wadda suke kallo tana kama da yin hasara a buga talla a jarida.
Mataimakin gwamna da Sakataren gwamnati da shugaban ma'aikatan jiha dana fadar gwamnati, ba su sanya taya murna a jaridu ba.
Kwamishinoni 31, daya ne kawai kwamishinan lafiya ya sanya a jaridar daily trust da Leadership.
Shugaban jami'a mallakar jiha da makarantar kimiya da fasaha ta Ummaru Ali Shinkafi da kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari suma ba  labarin sanya taya murna ga gwamnan ba ba za ka ce dai ba su san  muhimmancin hakan ba, don jagororin shaihunnan malamai ne.
Masu baiwa gwamna shawara da mataimaka na musamman da manyan daraktoci da manyan sakatarori da ke kallon kansu ma'aikatan gwamnati dukansu ba su yarda da hasarar taya murna ga Tambuwal a jarida ba.

Kakakin majalisa dake iya baiwa shugabannin mazaba baburan hawa a gaban Tambuwal kila bai fahimci buga taya murnar aika sako ne na nuna tare ga Gwamna a wurin abokan adawa da hamayarsa a jihohin Nijeriya kuma yana da bukatar hakan a wannan marrar.
'Yan majalisar jiha da tarayya sun kasa su yi ko da karo-karo ne su nunawa duniyar siyasar Nijeriya Tambuwal na da masu ƙara haskaka siyasarsa, ciki har da waɗanda ya yi wa riga da wando sun ki tun da ba saka hannun jari ne ba da zai hauhauwa bayan sauka kujera a riƙa ɗiba ana ci ba.
Jam'iyar PDP reshen Sakkwato sun bi sahu wajen ƙin sa hannu a haskaka tafiyar Tambuwal a wannan lokaci da ake buƙatar sanyawa tafiyar fetur da zai kara kunna wutar nasarar neman cigaba da rike gidan siyasarsa.
Managarciya ta fahimci da yawan muƙaraban Tambuwal sun san muhimmacin taya shi murnar sun dai ki yi ne a dalilin rowa da ta mamaye zukatansu, wasu daga cikinsu magoya bayansu sun rika yawo da tallar taya murnar da suka yi  a kafar sadarwa ta facebook domin haka ne mafi arha a yaɗawa, domin duk yanda aka yi maka tsada 1000 ta isa.

A lokacin da Tambuwal ke zagaye Nijeriya wajen gaisuwar Ta'aziya da buɗe aiyukka da wasu muhimman tarukka, amma mukarabansa sun kasa aikawa muhimman mutanen da yake zuwa wajensu saƙon cewa muna tare da namu ku ƙara goya masa baya. Wannan abin takaici ne ya faru, matuƙar Tambuwal bai samu damar daura wanda yake so ya gaje shi ba,  ya bayyana   wannan ranar  da muƙarabansa suka kasa baiwa muhimmanci ba za ta sake dawowa ba har abada.
Tambuwal ya yi shekara 57, muna fatan sake ganin wasu uku a tare da shi ko a lokacin zai samu makusanta ba irin wadan nan ba, ko da za su nuna jagoranmu yakai shekara 60.