Home Siyasa Tambuwal ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa Najeriya cikin ƙunci da rashin...

Tambuwal ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa Najeriya cikin ƙunci da rashin tsaro

17
0

Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙara ta’azzara matsalolin rashin tsaro, talauci da yunwa a faɗin Najeriya.

Tambuwal ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi ga wakilai a taron jam’iyyar ADC na jihar Sokoto.

A cewarsa, “Na yi imanin cewa ‘yan Najeriya sun riga sun gani da kansu abin da Bola Ahmed Tinubu zai iya kawowa, idan ma akwai wani abu da aka samu.”

Sanatan ya kuma yi zargin cewa ana samun rashin kyakkyawan tafiyar da dukiyar jama’a da kuma karkatar da ita, yana mai gargaɗin cewa irin waɗannan kuɗaɗe na iya zama hanyar sayen kuri’u a gabanin zaɓen shekarar 2027.

Ya ƙara da cewa tabarbarewar tattalin arzikin ƙasar na haifar da ƙaruwar rashin aikin yi da tsananin ƙunci, lamarin da ya ce ya gaza cika burin da ‘yan Najeriya ke da shi na shugabanci nagari.

Haka kuma, Tambuwal ya soki gwamnatin jihar Sokoto, yana mai cewa ta gaza cika muradin al’umma, duk da cewa bai bayar da cikakkun misalai ba.

Sai dai ya buƙaci mambobin jam’iyyar ADC da su kasance a haɗe tare da ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin ƙasa.

Ya kuma roƙe su da su kasance masu juriya da ƙwazo duk da abin da ya kira tsangwama daga jam’iyya mai mulki, yana mai cewa jam’iyyar za ta ci gaba da ƙarfafa tsarinta na ƙasa domin shirye-shiryen zaɓe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here