Tambuwal Ya Yi Nasarar Samun Kujerar Sanata

Tambuwal Ya Yi Nasarar Samun Kujerar Sanata

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya samu nasarar zana Sanata da zai wakilci yankin Sakkwato ta Kudu.

Tambuwal ya samu nasarar doke wanda yake saman kujerar Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba da tazarar kuri'a 4,976.

Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo jami'in tattara sakamakon zabe a yanki ya sanar da sakamakon zabe a garin Bodinga in da Tambuwal ya samu kuri'a 100,860.

Hakama ya sanar da Sanata mai ci Abdullahi Ibrahim Danbaba ya samu kuri'a 95,884.