Tambuwal Ya Tabbatar Da Mutuwar Mutum 15  A Hannun 'Yan Bindiga

Tambuwal Ya Tabbatar Da Mutuwar Mutum 15  A Hannun 'Yan Bindiga

Tambuwal Ya Tabbatar Da Mutuwar Mutum 15  A Hannun 'Yan Bindiga

'Yan bindiga da suka zagaye kauyukka hudu a gabascin Sakkwato sun kashe mutum 15 a daren Lahadi kamar yadda manema labarai suka samu labari.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a lokacin da yake gabatar da kasafin shekarar 2022 a ranar Litinin ya tabbatar da kashe mutanen.
"Bari na yi ta'aziya ga mutanen karamar hukumar Goronyo da Illela kan harin da aka kai masu jiya da dare in da aka kashe mutum 12 a Illela, uku a Goronyo."
A watannin nan Sakkwato na fama da hare-hare ana kashe mutane tare da ɓarnata dukiya.
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Illela Bello Isah Ambarura ya kauyukka uku ne aka kaiwa farmaki a yankin da suka hada da Kalmalu da Runji da Munwadata.
Ya ce Maharan sun yi garkuwa da wasu mutane da dama.
Shugaban ƙaramar hukumar Goronyo Alhaji Abdulwahab Goronyo ya ce mutum uku aka kashe an sace mata uku a harin.