Tambuwal ya sanya uwayen ƙasa biyu cikin majalaisar Sarkin Musulmi
Gwaman jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da nada uwayen kasa biyu cikin majalisar Sarkin Musulmi daga ranar 13 ga watan Satumba 2021.
A takardar da Sakataren majalisar Sarkin Musulmi Sa'idu Muhammad Maccido Danburam Sokoto ya sanyawa hannu ya bayyana sunayen uwayen kasar guda biyu da suka hada da Sarkin Kabin Yabo Alhaji Muhammadu Maiturare na biyu, uban kasar Yabo da Sa'in Kilgori Alhaji Muhammadu Jabbi Kilgori uban kasar Kilgori.
Bayanin ya sanarda cewa amincewar tana kunshe ne cikin takardar da babban sakatare a ɓanaren harkokin siyasa dake ofishin Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Abubakar Sahabi Bello ya sanyawa hannu.