Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambywal ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiyana dokar tabaci a dukkan yankunan da ‘yan ta’adda suka mamaye.
A cewar Tambuwal ya gana da shugaban kasa Buhari a fadar gwamnatin Nijeriya da marecen Litinin kusan minti 30 ya ce aiyanawar za ta karawa sojojin Nijeriya kaimi a hare-hare da suke kaiwa.
Kaddamar da hare-haren zai taimaka kwaran gaske a jihohin da batagarin suka addaba kamar Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja da Kebbi.
Tambuwal ya roki shugaba Buhari a samar da karin kayan aiki ga jami’an tsaro a dauki karin sojoji don ana da bukatarsu sosai.





