Tambuwal Ya Nemi Alfarma Ga Kwamitin Bincikensa Da Gwamnatin Sokoto Ta Kafa
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya nemi alfarma ga kwamitin da gwamnatin Sokoto ta kafa domin bincikar gwamnatinsa a tsawon shekara takwas.
Kwamitin binciken da gwamnatin Sokoto ta kafa ya aminta da alfarmar da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nema ta a sake sanya masa wata rana da zai bayyana gaban kwamitin ganin bai samu halarta a ranar Talata ba.
Gwamnan Sokoto Dakta Ahmad Aliyu ya kafa kwamitin binciken tsohuwar gwamnatin Sanata Aminu Waziri Tambuwal tsawon shekara takwas, ya ce ya kasa samun jirgin sama da zai dauko shi daga Sakkwato zuwa Abuja don fuskantar kwamitin.
Lauyan Tambuwal, Nuhu Adamu ya ce hakan ya taba faruwa a lokacin da aka kafa irin wannan kwamiti ga gwamnatin Attahiru Bafarawa bai bayyana ba, sai da aka saurari shedu gaba daya.
managarciya