Tambuwal Ya Karbi Wani Jigon APC Da Ya Koma PDP A Sakkwato
Gwamnan Sakkawato, Aminu Waziri Tambuwal, ya tarbi wani babban jigon APC reshen jihar, Alhaji Ɗahiru Maishanu Yabo, zuwa jam'iyyar PDP.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Yabo ya rike muƙamin kwamishinan yaɗa labarai da kwamishinan albarkatun ƙasa a baya lokacin mulkin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
Tsohon jigon APC ya samu tarba ta musamman daga gwamna Aminu Tanbuwal, mataimakin gwamana, Mannir Muhammad Dan Iya, da Sakataren gwmanatin Sakkawato, Muhammad Mainasara Ahmad.
Haka ma shugaban PDP a jihar Sakkwato, Alhaji Bello Aliyu Goronyo da wasu manyan jami'an gwamnati sun samu halartar taron karɓan jigon jam'iyyar adawa a jihar.
A wata sanarwa da mai baiwa gwamna Shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Bello, ya fitar, ta nuna cewa Yabo ya sauya sheƙa ne saboda rashin adalcin cikin gida a APC, da yawan alfarma.
Da yake jawabi, Yabo ya ce: "Jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato ta gina wata gwamnati ne da tilas ka zama mamba idan har kana so a tafi dakai a wurin kawo cigaba a ƙasa da kuma jiha."
managarciya