Tambuwal Ya Janye Dokar Hana Yawo A Sakkwato

Tambuwal Ya Janye Dokar Hana Yawo A Sakkwato
Gwamnan Jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) bayan tuntuɓar waɗanda ya kamata  ya bayar da umurnin ɗage dokar hana yawo da aka sanya a birnin Sakkwato  kwanan nan daga yanzu umarnin ya soma aiki.
Tambuwal ya duba ikon  da dokar kasa ta ba shi a sashe na 176, ƙaramin sashe na 2 na kudin tsarin mulkin ƙasa na shekara ta1999 da kuma sashe na 1 da na 2 da na 4 na dokar zaman lumana da kuma sashe na 15 na dokokin tabbatar da zaman lafiya na jahar Sokoto. 
 Gwamna ya buƙaci jama'a da mu cigaba da bin doka, mu kuma kasance masu kwaɗayin zaman lafiya a koda yaushe tare da nana ta buƙatar samun zaman lafiya a tsakanin al'ummar wannan jaha. Ya na mai jaddada muhimmancin zaman lafiya a wajen samar da kowane irin ci gaban al'umma. 
 
Kwamishinan yaɗa labarai Isah Bajini Galadanchi a sanarwar da ya fitar Jumu'a ya ce gwamnati ta haramta duk wani nau'in tarurrukan jama'a da ba su bisa ga doka a jahar, har sai yadda hali ya yi. 
Gwamna Aminu Tambuwal ya kuma bayyana godiyar sa ga Al'ummar jahar Sakkwato  kan fahimtar da sun ka nuna ta hanyar ɗa'a ga dokar hana yawo da aka sanya