Tambuwal Ya Baiwa Mutum 64 Mukami Domin Su Taimakwa Aikinsa Na Sanata
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya baiwa mutum 64 mukaman mataimaka na musamman da masu ba da shawara a bangarori daban daban na aikin majalisa dattijai da yake yi.
Sanata Tambuwal ya ba da mukaman ne ga 'yan asalin kananan hukumomi bakwai da yake wakilta a majalisar Dattijai.
Wannan yana cikin kudirinsa na samar da aiki ga mutanen yankinsa kamar yadda yake cewa.
Sanata Tambuwal ya nada masu bashi shawara 15, mataimaka na musamman a fannoni daban-daban guda 49 da suka fito a karamar hukumar Bodinga, Tureta, Dange Shuni, Tambuwal, Kebbe, Shagari da Yabo.
Tambuwal a takardar da ofishin yada labaransa suka fitar ya yi kira ga wadan da ya baiwa mukaman da su yi kokarin saukar da nauyin da aka daura musu.
managarciya