Tambuwal da 'yan Majalisar tarayya na PDP sun yi wa Wamakko ta'aziyar

Tambuwal da 'yan Majalisar tarayya na PDP sun yi wa Wamakko ta'aziyar
Sanata Aminu Waziri Tambuwal da sauran 'yan majalisar tarayya na PDP su huɗu da suka fito daga Sokoto sun ziyarci Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a gidansa dake Abuja domin jajanta masa kan rashin ɗan uwansa da ya yi a satin da ya gabata.
Sanata Tambuwal ya wallafa a turakarsa ta facebook ya ce "a yau, ni da abokan aiki na a Majalisar Dokoki ta kasa kuma jiga-jigan jam'iyyar PDP a Jihar Sakoto mun kai ziyarar ta'aziyya ga dan'uwanmu kuma abokin aikinmu, mai girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, tsohon Gwamnan Jihar Sakoto. 
"Mun kai ziyarar ne domin jajanta masa bisa rasuwar babban yayansa, Alhaji Liman Tambari Wamakko (Ubandoman Lokobi)," kalaman Tambuwal.
'Yan majalisar da suka raka Tambuwal akwai Abdussamad Dasuki da Mani Maishinko da Umar Yusuf Yabo da Honarabul Bashir Gorau.