Home Siyasa Tambuwal da wasu Sanatoci 8 Sun shiga ADC

Tambuwal da wasu Sanatoci 8 Sun shiga ADC

7
0

Akalla sanatoci tara daga jam’iyyu uku sun sanar da Majalisar Dattawa cewa sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC.

Sanatocin da suka bar Labour Party (LP) sun hada da Victor Umeh, Tony Nwoye da Ireti Kingibe.

Sauran biyar kuwa sun fice daga PDP, wato Aminu Waziri Tambuwal, Binos Yaroe, Lawal Adamu Usman, Mohammed Ogoshi Onawo da Augustine Akobundu.

Haka kuma Enyinnaya Abaribe daga APGA shi ma ya koma ADC, sai dai Majalisar Dattawa ta ba shi wa’adin mako guda ya sake nazarin matakin, tana mai cewa hujjar da ya bayar ta ficewa daga jam’iyyarsa ba ta cika sharuddan kundin tsarin mulki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here