Tambuwal Ba Ya Tallata Kansa---Gwamnan Jihar Delta Okowa

Tambuwal Ba Ya Tallata Kansa---Gwamnan Jihar Delta Okowa

Tambuwal Ba Ya Tallata Kansa---Gwamnan Jihar Delta Okowa

Gwamnan jihar Delta Ifanyi Okowa ya nuna kaduwarsa yanda ya ga Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal  na wasa da harkokin yada labarai da suka shafi sanar da  halin da yake ciki a gwamnatinsa.

Gwamnan Delta ya ce Tambuwal ba ya tallata kansa domin ya ga irin ayyukan da yake yi a jihar Sakkwato, kafin ya zo nan ba ya da wata masaniya kan ginin asibitin koyarwa ta jami’a  da ake yi wadda ba wata irinta a kasar Nijeriya.

Ya ce Makarantar mata ma da ake yi abu ne na yabawa musamman yanda tsarinta yake da ginin, ‘muna da bukatar irin wannan hobbasar a kasar Nijeriya don samar ilmi mai inganci da yanayi, kan wannan ka zama abin koyi da fatar gwamnonin Nijeriya za su koyi da kai,’ a cewarsa.

Ya kara da cewar ina baka shawara ka yi yanda mutane za su san abubuwan da kake yi a jiharka.