Tambuwal ba mutum ne da ya kamata duk wani dan siyasa ya bi ba------- Horabul Abdullahi Hassan

Tambuwal ba mutum ne da ya kamata duk wani dan siyasa ya bi ba------- Horabul Abdullahi Hassan
Tambuwal ba mutum ne da ya kamata duk wani dan siyasa ya bi ba------- Horabul Abdullahi Hassan< /div>
 
Daga Muhammad M. Nasir
 
Jigo a jam'iyar APC kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa Honarabul Abdullahi Hassan ya nuna mamakinsa kwaran gaske ya ga dan siyasa dake da mutane a bayansa har ya gamsu ya rika  tafiyar siyasar  Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.
Abdullahi Hasssan a zantawarsa da Managarciya ya ce Tambuwal ba mutum ba ne da yakamata dan siyasa ya bi ba, musamman a Sakkwato domin bai dauki 'yan siyasa da girma ba, ya a  je su ne kawai sai a lokacin zabe ya nuna maka muhimmancinka da lamarin ya kare kuma shikenan kowa ya kama gabansa, wanda hakan ba daidai ba ne ga dimukuradiyya.
'A tun lokacin da naga Gwamna Aminu Tambuwal ya tara 'yan siyasa kusan zaben kananan hukumomi yana tuna masu cewa  da kuka yi gwamnan mi kuka samu balle shugaban karamar hukuma, na fahimci a siyasa Tambuwal ba abin biya ba ne, kuma ni ba zan yi siyasarsa ba' A cewar Abdullahi Hassan.
Ya ce ka dubi shekara shidda Tambuwal na jagorancin Sakkwato ba abin da ya yi sai yanzu ya ciyo bashi yake aikin da ake yi yanzu, ba kudin ba aiki ba taimakon magoya bayansa, kuma yana kallon kansa a matsayin jagoran siyasa da har ake iya zaba shugaban kasa.
Honarabul ya karyata batun zai iya komawa PDP ya ce 'Ni ban sha'awar jam'iyar PDP kuma ina siyasa ne domin jama'a dukan magoya bayana sun gamsu da jam'iyar APC don haka ban fita daga cikinta sai dai in muka ga an yi kuskure za mu sanar da shugabanni domin a gyara ba don husuma ko kawo rabuwar kai ba.
Ko ka gamsu da zaben shugabanni da aka gudanar a satin da yagabata? ya ce ko kadan ban gamsu ba, domin kama karya ce aka yi a Sakkwato ba zabe ba.
'Wamakko kama karya  yake yi a jam'iyar APC bai bari a gudanar da siyasar cikin gida, matukar bai gyara ba akwai matsala a jam'iyar APC.
'In dai har Wamakko ne zai cigaba da jagorantar APC, Tambuwal na jagorantar PDP dukansu su tsayar da wadan da suke so a zaben 2023 akwai matsala a siyasar Sakkwato wadda dole ne a fito a yaki hakan don ceton jiha da al'umma gaba daya.