A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labarai ta bayyana cewa bincikenta ya gano cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya raba buhunan shinkafa 50 ga wasu zaɓaɓɓun ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Shafin ya yi iƙirarin cewa Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya bayar da tallafin ne ta hannun Honorabul Musa Bawa Yankuzo.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta Zamfara Newsletter, ta ƙaryata rahoton, tana mai cewa wani ƙoƙari ne na ƴan adawa domin su ɓata sunan tsohon gwamnan.
Kafar yaɗa labaran ta ce Yankuzo, wanda ake zargi da bayar da kayan ga ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindigan da ake nema ruwa a jallo, Ado Aleiro, a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, ya musanta zargin.
Wani na kusa da Yankuzo cikin wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng ya bayyana cewa: "Honorabul Musa Bawa Yankuzo ya bar ƙasar ne a ranar 5 ga watan Maris 2024 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a makon farko na watan Mayun 2024."
Kafar yaɗa labaran ta kuma bayyana cewa Abdullahi Headmaster wanda ake zargi da ajiye shinkafar ya musanta zargin.
Rahotanni sun bayyana cewa yana tuntuɓar lauyoyinsa domin kai ƙarar shafin yaɗa labaran.
Jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma ta yi barazanar shiga kotu da jam'iyyar PDP a jihar Zamfara. APC na kalubalantar PDP kan zargin da ake yaɗawa cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya raba kayan abinci ga 'yan ta'adda.
Jam'iyyar ta kalubalanci PDP da ta kawo shaidu kan zargin da ta ke yi ko kuma ta fuskanci shari'a a kotu, cewar Tribune.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yanki na jam'iyyar, Musa Mailafiya Mada ya fitar a Kaduna. Mada ya ce su na maraba da adawa mai amfani amma bai kamata ya wuce gona da iri har da kokarin bata suna ba.