Ta'addanci Bai Hana Noma Ba A Najeriya-----Ministan Noman Najeriya

Ta'addanci Bai Hana Noma Ba A Najeriya-----Ministan Noman Najeriya

Ministan Ayyukan Noma a Najeriya Mohammed Abubakar ya ce, ayyukan ta’addancin da kasar ke fuskanta ba su shafi ayyukan noma da samar da abinci ba.

A rahoton wanda gidan talabijin na Channels TV ya wallafa Ministan ya amince da cewa rashin tsaro ya na hana manoma shiga gonakinsu, musamman a yankin Arewa wanda hakan abin damuwa ne ga gwamnatin tarayya.
Ya ce, duk da haka, ana ci gaba da samar da abinci ba tare da wata matsala ba a wasu sassan yankunan kasar.
Ministan ya ci gaba da bayyana cewa, an samar da ayyuka kai tsaye daga kudin tallafin harkar noma na dala biliyan 1.1 da kasashen waje suka ba Najeriyar.
A cewarsa, Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya amince da ba da tallafin dala miliyan 538 domin a samar da shiyyoyin sarrafa noma na musamman a Najeriya.
Bankin ya baiwa jihohin da suka halarci taron kamar su Akwa Ibom, Bauchi, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Kebbi, Ogun, Ondo, Oyo, Plateau da Sokoto.
Ministan ya kuma karyata rahotannin baya-bayan nan da ke cewa Najeriya ba ta kan hanyar kawo karshen yunwa nan da shekarar 2025.
Abubakar ya bayar da misali da yadda Najeriya ke samar da wadataccen abinci wanda ya sanya kasar a matsayi na daya a nahiyar Afirka, kuma ta 4 a duniya wajen noman shinkafa.
Abubakar ya kara da cewa hakan ya nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ke kan gaba wajen cika alkawarin da ya yi na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru goma.