Sunayen Gwamnonin APC Da PDP Da Ake Zargi Da Rashin Cikakkun Takardun Makaranta

Sunayen Gwamnonin APC Da PDP Da Ake Zargi Da Rashin Cikakkun Takardun Makaranta

 

Da yawa daga cikin ‘yan siyasar Najeriya sun shiga cikin rigingimu na satifiket ɗin kammala karatu ko na bautar ƙasa, wanda hakan ya janyowa wasunsu rasa kujerunsu. 

Misali, tsohuwar ministar kuɗi, Kemi Adeosun, wacce ta yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta rasa muƙaminta saboda rashin gabatar da sahihin satifiket ɗin bautar kasa wato NYSC.
Haka nan, an kori jam’iyyar APC daga zaɓen gwamna na 2019 a jihar Bayelsa, lokacin da aka samu mataimakinsa da takardu na bogi. 
A yanzu haka wasu gwamnonin APC da na PDP sun faɗa cikin irin wannan bahallatsa, kuma ana ta cece-kuce a kai.
A yanzu haka Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, wanda ɗan APC ne, yana fuskantar shari'a a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe dangane da sakamakon jarabawar sa ta WAEC. 
A ranar Laraba ne wata ƙungiya ta bai wa WAEC wa’adin sa’o’i 48 da su gabatar da sakamakon Sanwo-Olu ko kuma a yi ƙararsu. 
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan da ya gabatar da sakamakon jarabawarsa ta WAEC ga jama’a, domin tabbatar da adalci kamar yadda The Guardian ta wallafa. 
A nasa bangaren, gwamnan jihar Enugu na fama ne da rigimar satifiket ɗin NYSC a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke jihar Enugu. 
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour ne ya shigar da ɗan takarar na PDP da ya lashe zaɓen ƙara a gaban kotu. 
Hukumar ta NYSC ta ce satifiket ɗin da gwamnan ya bai wa hukumar zaɓe wato INEC, ba ita ce ta buga shi ba kamar yadda Sahara Reporters ta kawo. 
A Sakkwato jam'iyar PDP na zargin mataimakin Gwamnan jihar Idiris Muhammad Gobir da rashin kammala makarantar Furamare in da suke kalubalantar hakan a gaban kotu.