SSS sun kama wani dan jarida ya na sauka a filin jirgin sama na Legas 

SSS sun kama wani dan jarida ya na sauka a filin jirgin sama na Legas 

Jami'an tsaron farin kaya na SSS sun kama dan jaridar nan, Adejuwon Soyinka jim kadan bayan isowarsa Nijeriya.

Premium Times ta rawaito cewa an kama Soyinka ne a filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammad dake Legas.

Dan jaridar, wanda tsohon ma'aikacin BBC ne, an tsare shi da misalin karfe 5.40 na safe.

Premium Times ta rawaito cewa kawo yanzu dai ba a bada dalilin tsare shin ba.

Abokan aikin dan jaridar, wanda lashe kyaututtuka da dama sun ce ba a samun sa idan an kira wayarsa.