Hukumar kula da yanayi ta NiMet ta fitar da gargaɗi cewa jihohi 11 na Arewa, ciki har da Kano da Sokoto, na cikin haɗarin fuskantar barkewar cutar sankarƙau yayin da yanayin bushewar kakar rani ke ƙaruwa.
Sanarwar ta ce cutar sankarƙau tana shafar abubuwan da ke bayar da kariya ga kwakwalwa da kashin baya, kuma mafi yawan lokuta tana faruwa ne sakamakon kwayar cutar Neisseria meningitidis.
Hukumar ta bayyana cewa cutar na yaduwa ta hanyar numfashi, musamman a wuraren cunkoson mutane ko inda iska ba ta isa sosai.
NiMet ta lissafa Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe, da Borno a matsayin jihohi masu haɗari fuskanatar barkewar cutar sosai.
Haka kuma, ta shawarci mazauna tsakiyar ƙasar su kasance masu lura da kai rahoton alamun cutar da wuri, yayin da Plateau, Oyo, Cross River, Edo, Ekiti, da Enugu aka sanya a yankunan da ba su fuskantar haɗarin cutar sosai.
Hukumar ta bayyana cewa yara, matasa da mutanen da ke zaune a wuraren cunkoso da waɗanda ke fuskantar yanayin bushewa da ƙura, da masu rauni a garkuwar jiki sune wadanda suka fi hadarin kamuwa da cutar.
NiMet ta lissafa alamun cutar kamar zazzabi mai ƙarfi, ciwon kai sosai, ciwon wuya, amai ko tashin zuciya, da jin zafi sosai.
Najeriya ta sha fama da barkewar sankarƙau a shekaru da dama, musamman a jihohin Arewa.





