Sokoto da wasu jihohi uku dake cikin hadarin kamuwa da cutar Sanƙarau
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, Nimet ta lissafo wasu jihohi a ƙasar da suke cikin haɗarin kamuwa da cutar sanƙarau.
A shafinta na X, hukumar ta Nimet ta ce jihohin da suka fi haɗari galibi a yankin arewacin ƙasar ne da suka ƙunshi Sokoto da Jigawa da Yobe da Borno.
Jihohin da suma suke cikin haɗarin ɓullar cutar sun haɗa da Zamfara da Katsina da Kano da Bacuchi da Gombe da Kebbi da Adamawa.
Bayanin na Nimet na zuwa daidai lokacin da a baya-bayan nan hukumomi a jihar Yobe suka tabbatar da ɓullar cutar ta sanƙarau a makarantun sakandaren mata uku da kwalejin ƴan mata ta gwamnatin tarayya a ƙananan hukumomin Potiskum.
Cutar ta yi ajalin ɗalibai 17 ƴan makarantar kwana yayin da ragowar ukun ƴan Firamare ne sai kuma wasu da dama da suke jinya a asibiti sakamakon kamuwa da cutar ta sanƙarau.
A asibitin ƙwararru na Potiskum, an samu adadin mutum 214 da suka kamu da cutar sannan uku kuma suna cikin sashen kula da lafiya na asibitin suna karɓar magani.
A bayanin na Nimet, akwai jihohin da ke da sauƙin kamuwa da cutar da suka haɗa da Kaduna da Filato da wani ɓangaren Adamawa da Neja da Kwara da Abuja da Nassarawa da Taraba da Benue da Kogi.
Sai kuma jihohin da ba sa cikin haɗarin kamuwa da cutar ta sanƙarau da suke yankin kudancin Najeriya.
A wannan maƙalar za mu duba alamomin cutar ta sanƙarau da kuma yadda mutum ke iya kare kansa daga ita.
Farfesa Sadiq Isa, masani kan lafiyar iyali ya shaida wa BBC cewa sanƙarau cuta ce da ke iya shafar ƙwaƙwalwa da laka.
Ya kuma ce alamomin cutar ta sanƙarau na iya zama bai ɗaya sannan a wasu lokutan suna iya bambanta a jikin waɗanda suka kamu da ita.
A cewarsa, alamomin cutar sun haɗa da:
- Zazzaɓi
- Ƙagewar wuya
- Matsanancin ciwon kai
- Tashin zuciya
- Shiga yanayin kasa tsugune ko tsaye
- Fitar hayyaci
- Jijjigar jiki kamar farfaɗiya
- Gujewar haske ko na rana ko fitila.
- Masanin ya ce akwai illolin da wannan cuta ta sankarau za ta iya yi ga lafiyar wanda ya kamu da ita.
-
Ya lissafo illolin kamar haka:
- Lalata ƙwaƙwalwa baki ɗaya wanda hakan na iya jefa mutum cikin haɗarin rasa rai
- Suma
- Shanyewar ɓarin jiki ko rashin karfin hannaye da ƙafafu
- Rayuwa da cutar farfaɗiya
- Cutar mantuwa
- Watsuwar ƙwayar cutar zuwa ɓangarorin jiki
- Kurmancewa ko makancewa ko bebancewa
-
Farfesa Sadiq Isa ya ce babbar hanyar kariya daga cutar sanƙarau ita ce yin rigakafi.
Don haka ya buƙaci hukumomi su samar da isassun alluran a kan lokaci yadda mutanen da ke buƙata za su samu.
Sannan kuma a cewarsa, ya kamata mutane su je su yi rigakafi domin samun kariya ba sai lokacin da aka samu ɓarkewar cutar ba.
Ya kuma yi magana kan tabbatar da tsaftar jiki - yawan wanke hannu da kuma kiyayawa wajen yin attishawa da tari a kusa da wasu saboda galibi cutar na yaɗuwa ne ta iska.
Masanin ya kuma tunasar a kan makarantun kwana da sansanonin gudun hijra inda ake da mutane da dama da ke zaune a wuri lokaci guda.