Sojojin Nijeriya Sun Yi Nasarar Kashe Kasurgumin Dan Bindiga

Sojojin Nijeriya Sun Yi Nasarar Kashe Kasurgumin Dan Bindiga

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi ƙarin haske kan yadda ta ce dakarunta suka kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Janari, da mabiyansa da dama a wani sumame da suka kai ƙarƙarshin rundunar tabbatar da tsaro ta Operation WHIRL PUNCH.

Rundunar ta bayyana cewa ta yi nasarar kawar da ɗan bindigan ne yayin da ya ke tattara maƙarrabansa da niyyar kai hari a maɓoyarsu da ke ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, a arewacin Najeriyar.

Kakakin rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya shaida wa BBC cewa rundunar ta sami nasarar ne bayan ta ɗauki lokaci tana dakon gungun 'yan bindigan kafin suka yi dace suka yi arangama da su a yankin Gadar Katako da ke ƙaramar hukumar Igabi.

'Lamarin ya auku ne a ranar 18 ga watan Janairu, amma sai bayan 'yan kwanaki muka sami tabbacin cewa an kashe wannan ɗan bindiga da mabiyansa. Shi wannan mutumin Janari mun sami labarin cewa yana da hannu cikin harin da aka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna', kuma muna da tabbacin cewa yana da hannu a cikin hare-haren da ake kaiwa a hanyar Abuja zuwaAir Vice Marshal Gabkwet ya ƙara da cewa dangane da irin miyagun ayyukan da 'yan bindiga irinsu Janari ke aikatawa akwai buƙatar a ɗauki tsauraran matakai a kansu a duk lokacin da dama ta samu.

Ya ce akwai buƙatar ganin cewa an sami haɗin kai daga duk ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki a harkar tsaro domin a samu damar magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Ya ƙara da cewa 'Ita wannan harka ta 'yan bibdiga, ba wai za ka ce idan ka kashe duka shugabanninsu shikenan abin ya ƙare ba, mu dai za mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu na soji, amma dole ne a magance matsalolin da ke bai wa waɗannan mutane damar jawo hankalin ƙananan yara da suke tattarawa cikin mabiyansu. Sojoji za su yi nasu, jama'a ma su yi nasu, da kuma gwamnati a kowa ne mataki. Kaduna.' In ji shi.