Sojojin Nijar  sun Sanar Da juyin mulki a Kasar

Sojojin Nijar  sun Sanar Da juyin mulki a Kasar


Sojoji sun sanar da karɓe iko a Nijar a hukumance.

Wasu sojoji ƙalilan ne suka fito gidan talabijin na ƙasar suka tabbatar da juyin mulkin da suka yi.

Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar, sannan kuma sun kulle duka iyakokin ƙasar baki ɗaya.

Babu dai labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki ya zuwa yanzu.

Amma sojojin sun bayar da sanarwar sun tuɓe shi daga muƙaminsa.

Sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziƙi.

Shugaban ƙasar Benin Patrice Talon wanda ke jagorantar tawagar ECOWAS na cikin ƙasar, sai dai sun gaza cimma wata yarjejeniya da masu gadin shugaban ƙasar da suka amshe mulkin.

Tun a safiyar jiya Laraba ne aka bayar da rahotannin tsare Shugaba Bazoum a gidan gwamnati, abin da ya janyo zanga-zanga daga magoya bayan Bazoum.

Sojoji sun yi harbe-harben jan kunne domin tarwatsa masu zanga-zangar.