Sojoji sun kuɓutar da mata 5 da jarirai 2 daga hannun ƴan ta'adda a jihar Neja
Dakarun 'Operation Hadarin Daji' da ke dajin Kuyambana a jihar Zamfara sun ceto jarirai biyu da mata biyar da aka sace daga kauyen Marange da ke karamar hukumar Kagara a jihar Neja tun a watan Janairun 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na 'Operation Hadarin Daji', Laftanar Suleiman Omale ya fitar.
Omale ya ce an kubutar da su ne ta hanyar farmakin da sojojin suka kai a daukacin yankin Kuyambana a jihar Zamfara.
“An yi nasarar ceto mutanen ne sakamakon matsin lamba da sojojin suka yi wa ‘yan bindigar, wanda ya sanya waɗanda aka sace din su ka tsere daga yankunan ‘yan ta’addan.
"Sun shaki iskar yanci daga ranar 13 ga Maris, 2024 lokacin da sojojin suka kubutar da su " in ji shi.
managarciya