Sojoji Sun Durfafi 'Yan Ta'addan Lakurawa, Sun Samu Tarin Nasarori

Sojoji Sun Durfafi 'Yan Ta'addan Lakurawa, Sun Samu Tarin Nasarori

Rundunar sojojin Najeriya ta musamman ta yi nasarar fatattakar ƴan ta'addan Lakurawa da dama. Rundunar sojojin ta kuma lalata sansanoni kusan 22 na ƴan ta'addan a jihohin Sokoto da Kebbi. 
Babban kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele, shine ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a a Sokoto. 
Ya bayyana hakan ne ta bakin muƙaddashin babban kwamandan runduna ta 8, ta sojojin Najeriya dake Sokoto, Birgediya Janar Ibikunle Ajose. Soyele ya ce, babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa ne ya tura rundunar ta musamman domin gudanar da aikin. Ya ƙara da cewa an samu nasarorin ne ta hanyar sababbin hare-hare da aka kai kan ƴan ta'addan Lakurawa, wanda ya kai ga lalata sansanoninsu. Ya kuma umarci sojojin da su tabbatar da lalata ƴan ƙungiyar ta Lakurawa, sannan ya buƙace su da su bi ƙa’idojin aiki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Soyele ya ƙara da cewa wannan aiki na musamman, ana yinsa ne domin tabbatar da ganin an kawar da ƴan ƙungiyar Lakurawa gaba ɗaya a jihohin Sokoto da Kebbi. 
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu gudanar da ayyukan yaƙi da ta'addanci sun kashe ƴan ta'adda aƙalla 181 a cikin makon da ya gabata. Dakarun sojojin sun cafke masu laifi 203, da suka haɗa da ɓarayin mai guda 50, tare da ceto mutane 161 da aka yi garkuwa da su.