Sojoji a  Neja sun hallaka 'yan bindigan da suka gudo daga Zamfara

‘Yan bindigar, waɗanda aka ce ɗaruruwan su ne suka tsere daga  dajin Allawa sun afka sansanin sojoji dake dajin inda suka yi ruwan wuta fito na fito da sojoji, artabun da ya ɗauke su tsawon awanni.

Sojoji a  Neja sun hallaka 'yan bindigan da suka gudo daga Zamfara
Sojoji a  Neja sun hallaka 'yan bindigan da suka gudo daga Zamfara
Sojoji a  Neja sun hallaka 'yan bindigan da suka gudo daga Zamfara
‘Yan bindiga da ke ƙokarin tserewa daga jihar Neja biyo bayan luguden wuta da suke sha a jihohin Zamfara da Katsina sun gamu da ajalin su a hannun sojoji a ƙauyen Maganda kusa dajin Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
‘Yan bindigar, waɗanda aka ce ɗaruruwan su ne suka tsere daga  dajin Allawa sun afka sansanin sojoji dake dajin inda suka yi ruwan wuta fito na fito da sojoji, artabun da ya ɗauke su tsawon awanni.
An kuma gano cewa an kashe da dama daga cikin 'yan bindigar yayin da wasunsu suka tsere cikin dajin da munanan raunukan harbin bindiga da harsasai cikin jikinsu,  an ce Sojoji sun kewaye dajin baki ɗaya.
An ƙwato manyan bindigogi guda shida da wasu ƙirar AK-47 da buhunan alburusai daga hannun ɓarayin.
Wata majiya a yankin Allawa ta ce, “A gaskiya daga gawarwakin da muka gani, dukkaninsu ba su yi kama da 'yan Najeriya ba domin suna ɗauke da dogon gashi akan su kamar mata. Ba su da kamannin ‘yan Najeriya sam kuma daga dukkan alamu basu san akwai sansanin sojoji a dajin ba hakan ya ba da damar yi masu ƙofar raggo.
Daga Yushau Garba Shanga.