Sirrukan Da Ke Tattare Da Miyar Egusi

Sirrukan Da Ke Tattare Da Miyar Egusi

Aisha Bashir tambuwal

aishabasheer2017@gmail.com

 

Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu, uwargida da amarya da dukkan masu bibiyar wannan kafa ta yada labarai wato MANAGARCIYA ina yi maku ku barka da warhaka. 

To a yau dai na kawo muku yanda ake miyar Egusi, dafatar za ku biyoni domin ganin yanda za'a haɗa wannan miyar mai matukar tasiri da wasu sirruka.
 
       *Miyar egusi* 
 
 *Abubuwan da ake bukata:-* 
 
Egusi
Kayan miya
Ganyan ogun/alayyahu 
Manja
Ganda/nama/kifi
Maggi
Kayan kamshi
 
 
 
 
    *Yanda zaki hada* 
 
Za ki samu naman mai kyau  ko kifi (idan kifin kike da bukata) ki gyara ki ajiye a gefe,sai ki dauko kwano ki kwaba egusi da ruwa kwabin yayi kamr za ki yi kosai,sai ki dauko pan dinki ko tukunya ki dora a wuta ki zuba manjan ki ,in ya yi zafi sai ki dinga soya egusin naki kaman  yin kosai ,kina juwa in ya soyu sai ki kwashe ki zuba kayan miya akan mai din ki rufe,ki bar kayan miyan ya dahu sannan sai ki zuba maggi da nama , in suka dahu, ki saka kayan kamshi,sai ki dauko wa  nn egusi  din da kika soya sai ki zuba aciki,ki rufe zuwa 'yan  mintuna sai ki juya, zaki ga miyar taki tayi kyau kuma egusin ya dan dunkule, in kina bukatar kifi a ciki sai ki saka, ko kayan ciki duk anasawa, sai ki zuba ganyan ogun dinki,in babu ki saka alayyahu kadan, ki rage wutar, ki rufe zuwa minti 2-3 sai ki sauke ki kwashe, za ki ga man miyar  ya fito, kuma ta yi kyau saboda egusi din duk ya dunkule.
 
 Anaci da tuwon shinkafa,semo,amala, sakwara.
 
 *Ɗan tsokaci* 
 
Amfanin soya egusi din nan shi ne za ki ga miyar tayi kyau, kuma ta dunkule ta hada jikinta kuma gaskiya miyar egusi tanason kayan dandano, nama, kifi, ganda, kayan ciki duk kana iya saka su duka aciki wuri guda.
    Miyar Egusi tana da sirruka daban-daban wanda ita kadai take da su, kadan daga cikinsu: 
Miya ce ta wadata,
Miya ce ta gwanayen mata a girki,
Miya ce ta kece reni,
Miya ce ta alfarma.