Sirrin Waina ko Masar shinkafa da sauran abincin Bahaushe ba ya da shi 

Sirrin Waina ko Masar shinkafa da sauran abincin Bahaushe ba ya da shi 

 

 

 

                                             WAINA KO MASAR  SHINKAFA

                                                 Aysha Basheer tambuwal

 

Kayan hadi

-farar shinkafa

-yis

-nono

-sukari 

-albasa idan ki na bukata


Yanda ake yin ta

 Da farko dai uwar gida za ki sami danyar shinkafa mai kyau da tsafta, ki jika ta a ruwa ta yi minti goma ko sha biyar ko rabin awa, sai ki wanke ta, ki kai injin a markada miki, kuma kar ki bari a zuba ruwa cikin markaden, idan shinkafar rabin mudu ce kisa yis cokali (1) kisa nono kadan, sai ki buga ta sosai ki rufe, ki kai ta wurin zafi inda za ta yi saurin tashi, idan ta tashi sai kisa gishiri da sukari daidai yanda kike son dandanon.

   Sai ki dauko  dafaffiyar shinkafa ki zuba, ita ma yanda kike bukatar ta a cikin kullun masar ki, ana  yanka albasa in ki na so a ciki, sai ki koma bugawa ko juyawa ko motsawa sosai , sai ki dora tanda a kan wuta ki zuba mai, idan man yayi zafi sai ki dinga debo kullun a ludayi kina zubawa a tandar.

  Idan ki ka bar bari daya ya soyu sai ki juya bari dayan, idan ta soyu sai ki kwashe ki sa takarda   a akushi (food flask)  sai ki zuba masar a ciki kar ta huce, kafin ki gama suya sai ki rufe saman da takardar sannan kisa murfi ki rufe, haka za ki yi har ki kammala. Ana cin masar da miyar ganye ko miyar agushi, ko taushe ko romo irin wanda ke sa mai gida santi.

Amfanin Masa ko Waina a jikin Dan adam

   Masa kamar yadda aka sani abincin Bahaushe ne da ya gada kaka da kakanni, in da wasu ke gani ya samo abincin ne a wurin Larabawa a cudanyar sa da su a lokacin kasuwanci tun kafin karbar musulunci. Bayan ganin abincin a wurin su ya karba ya mayar da shi abincinsa, kamar sauran abincin da aka same shi ya na ci tun asali.

    Masana kiyon lafiya sun tabbatar da waina ko masa abinci ce, mai sanya kuzari kamar sauran dangin abinci irinsu tuwo shinkafa da masara ko rogo.

Sirrin Masa da sauran abincin Bahaushe ba ya da shi 

 1. Masa ce kadai abincin da maza ba su yi komai gwanintar iya abincin su. 
 2. Waina ko masa ita ce abincin da Bahaushe ya dauka duk gidan da ka ganta ana ci akwai wadata a gidan.
 3. Masa ce kadai ba a shakkun  baiwa kowa ita a ko'ina, domin ita ta na cikin jerin abincin Bahaushe na marmari. 
 4. An camfata da cewa duk san da mutum ya ci masa ta sanya shi kuraje a jikin sa, to haka abun zai bi shi duk ya ci wainar  sai ya yi kurajen.
 5. Kayan hadin masa dukkan su dole ne a tanade su, wani baya isarwa wani sabanin sauran abincin Hausawa.  
 6. Sukari da gishiri ba su haduwa wuri daya, har su samar da dandanon da ake bukata, amma masa ta kan adana su wuri daya tare da gamsar da mai ci. 
 7. Masa ce abincin na musamman da ya dade kasar Hausa, amma ba kowace mace ke iya yinta ba.
 8. Hausawa na girmama Waina fiye da sauran dangogin abinci, wanda hakan ya sanya duk bikin da ba su ganta ba, sukan dauki bikin bai kammala ba a bangaren abinci. 
 9. Masa na cikin abincin da Bahaushe ke neman biyan bukata da ita, watau (sadaka). 
 10. Masa na cikin abincin da Hausawa ba su walakantawa, kuma ba su yin almubazzaranci da ita, kan haka har camfin gargadi suka kirkiro wa yara kanta "duk yaron da ya goge kashi da masa zai zama biri".

Ma su karatu da fatan kun ilmantu da abin da ku ka karanta kan girkin Masa, in haka ne sai ku biyo ni wani lokacin don jin wani girkin Bahaushe.