Sirrin Mu Mata:Kaɗan Daga Cikin Aiyukkan Man KWAKWA

 Sirrin Mu Mata:Kaɗan Daga Cikin Aiyukkan Man KWAKWA

SIRRIN MU MATA GROUP
 
 
Taushin fata – Ana iya shafawa kamar man jiki a shafa a ko’ina har wuya.
Man fuska – ana shafawa a zagaye ƙwayar ido da shi yana maganin baƙin da ke fitowa zagaye da ido, yana kuma maganin tamushewar fata na tsufa.

Kwantar da fata yayin aski – Man Kwakwa yana gyarawa masu aski, kamar maza masu yawan yin kurajen fuska, sakamakon gyaran fuska da sauransu, yana warkar da kuraje.
Man goge hakora – akwai magungunan wanke baki dayawa amma wannan na daban ne ku hada man Kwakwa da ‘Baking Soda’ a gauraya don kadan a sa a ‘Brush’ a goge baki da shi.

Ana shafa man Kwakwa kadan a jikin auduga a goge fuska da shi yana gagawan cire kwalliyar da ta dankare a fuskar mata.
Yana hana fashewan lebe, musamman a lokacin sanyi ba.
Man Kwakwa yana gyara jikin jarirai, musamman ma irin masu yin ciwon Ella din nan har cikin gashin kansu, ana ganin kokon kai yana yi kaman Amosani fari fat, to uwa ta dage da gogawa yaro man Kwakwa insha Allahu zai warke.
Yana gyara gashin mata, yana sasu kara karfi, yana kashe amosani sannan yana kashe kwarkwata.
Yana maganin cututukan fata da dama, kamar su Eczema, kunan wuta, kyasbe da dai sauran cuttukan fata.

Ana iya hada man Kwakwa da suga a murza a fata, sannan a wanke da ruwa da sabulu yana sa fata ya yi laushi lukwi-lukwi da shi.

MRS BASAKKWACE