SINASIR NA SEMOVITA:Hadin Na Musamman A Lokaci Na Musamman

SINASIR NA SEMOVITA:Hadin Na Musamman A Lokaci Na Musamman
BASAKKWACE'Z KITCHEN
 
 
 
SINASIR NA SEMOVITA:Hadin Na Musamman A Lokaci Na Musamman
 
 
INGREDIENTS
Semovita
suga
yis
ruwa
gishiri
mai
 
METHOD
Aunty na za ki kwaɓa semovitan da yis kamar kwaɓin fanke sai ki barshi ya tashi kamar 30minutes, sannan ki ɗauko ƙullun ki ɗan ƙara masa ruwan sanyi ya yi dai-dai ƙullun waina sai ki sa masa ɗan gishiri da suga ki juya sosai idan kina son albasa za ki iya sawa.
Sai ki ɗora kaskon suyar sinasir ɗinki, ki fara suyar ki zuba mai, sai ki zuba kullun ba a juyawa har ya soyu amma idan kina so za ki iya juyawa tunda na semovita ne.
Shikenan kin gama za ki iya ci da komai.
Wannan hadi ne na musamman a lokaci na musamman, za ki tabbatar da haka a lokacin da ki ka shiryawa iyalanki wannan don za ki ji kalaman su kan girkin ba zai tsayu kawai ga godiya ba har da neman alfarmar ci gaba da yi masu irin wannan hadin.
 
 
MRSBASAKKWACE