Sinadarin Girki Dashishi

Sinadarin Girki Dashishi

BASAKKWACE'Z KITCHEN


       DASHISHI 
 
METHOD
Alkama
Kayan miya
ayan Lambu
Kifi Da nama idan da hali
magg
gishiri
curry
mai

 
METHOD
A surfa miki alkama a wanke a tsane ta bushe akai inji a barza, ki tankade da tsakin zakiyi amfani. ki turara tsakin bayan kin yayyafa ruwa kaɗan.
bayan minti talatin ki sauke ki tafasa nama da kayan ɗanɗano ki yanka gutsi gutsi ki gyara busasshan kifin ki ki zuba akan tsakin da kika turara shi da nama da kika yanka gutsi gutsi, ki yanka karas da kabeji. green pies,da Albasa sai ki zuba a kai ki zuba markadadden kayan miyan ki akai amma ba da yawa ba yadda zai jika tsakin ba, ki sa maggi, gishiri, da curry, ki juya sossai, ki mayar kan wuta ki kuma turarawa, idan yayi laushi sai ki sauke, idan yayi tauri ki yayyafa ruwa. yana da dadi zaki burge mai gida da shi, zaki iya yiwa masa a matsayin tuwon rana ki hada masa da salad ɗin hanta da lemon kan kana. ranar sai ya baki lambar yabo

 
MRSBASAKKWACE