Shugabannin  PDP Sun  Shiga Ganawar Sirri Da 'Yan Takarar Gwamnoninsu 

Shugabannin  PDP Sun  Shiga Ganawar Sirri Da 'Yan Takarar Gwamnoninsu 

 
Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga ganawar sirri da yan takarar gwamna karkashin tutarta a fadin jihohin Najeriya 36.
Dukkan yan takarar kujeran gwamna na PDP ke hallare a zaman illa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da na Bauchi, Bala Mohammed AbdulKadir, rahoton Leadership.
Yayin Bala Abdulkadir ya bada hakurin cewa yana kan hanya, Seyi Makinde na birnin Landan inda suka je ganawa da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu. An yiwa zaman take taron tattaunawa tsakanin shugabannin uwar jam'iyya da yan takara a zaben 2023.
Wannan ganawa na zuwa ne daidai lokacin da ake kira ga Shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, yayi murabus bisa sharadin da Wike da mabiyansa suka gindayawa PDP don sulhu tsakaninsa da Atiku.