Shugaban PDP Ya Yi Magana Kan Zargin Karbar Rashawar Biliyan Daya Da Wike Yake Masa

Shugaban PDP Ya Yi Magana Kan Zargin Karbar Rashawar Biliyan Daya Da Wike Yake Masa


Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya tabbatar da cewa ya karba N100 miliyan daga wani Gwamna. 

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi shugaban jam’iyyar na kasa da laifin rashawa inda yace baya da N100 miliyan da ya karba daga Gwamnan, Ayu ya karba N1 biliyan daga ‘dan takarar shugabancin kasa a Legas, Daily Trust ta rahoto.
A yayin amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala taron yardaddu na jam’iyyar a hedkwatarta dake Abuja, Ayu yace batun N1 biliyan ya fara ne tun bayan da ya hau kujerarsa ina yana neman kudin rike kasa. 
Yace jam’iyyar ta so karbar bashi amma an dakatar da hakan inda ya bayyana cewa bai karba wani kudi ba a matsayinsa na shugaban jam’iyyar na kasa. 
A kan batun zargin N100 miliyan, Ayu yace kudin da ya karba daga Gwamnan PDP an yi amfani da su ne wurin gyara People’s Democratic Institute wacce za a kaddamar a cikin kwanakin nan. Yace kudin basu kare ba kuma ya aike da wasika ga gwamnan da ya zo ya ga yadda aka yi amfani da kudin.