Shugaban Majisar Dattawa ya yi wa mutane 15 afuwa daga gidan yari a Yobe
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Sakamakon alfarmar watan Ramadan, shugaban Majisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya biyawa daurarru 15 bashi a gidan gyaran hali a dske garin Gashu'a, shalkwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe.
Wadanda suka ci gajiyar afuwar, bayan yanke musu hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru daban-daban, sakamakon bashin da ake bin su, daga kananan hukumomin Yusufari mutum 4, Jakosko mutum 3, yayin da sauran suka fito ne daga Potiskum da Bursari a jihar Yobe.
Baya ga haka kuma, Sanata Ahmed Lawan ya bai wa kowane daya daga cikin su kyautar naira 50,000 da yadin shadda 10 domin su koma cikin iyalin su tare da gudanar da ayyukan ibadar watan Ramadan.
Da yake jawabi a madadin Shugaban Majisar Dattawan, shugaban karamar hukumar Bade, Mallam Ibrahim Babagana ya ce sun gudanar da wannan aikin jinkan bisa umurnin Sanata Ahmed Lawan, a matsayin jinkai ga mutanen wadanda dukan su bashi ne ya kai su gidan gyaran hali.
"Duk da ba iya adadin da ya bamu umurnin ayi wa afuwar ba, ya ce mu biyawa wadanda ake bi bashin, amma sauran laifukan ba zai tsoma baki a kai ba. Al'amarin da ya jawo wannan adadi na mutum 15 ne kadai muka samu a nan gidan gyaran hali dake Gashu'a."
Hon. Babagana ya kara da cewa, "Akalla ya kashe sama da naira miliyan uku (N3m) wajen yanto wadannan mutanen, kuma ya tallafa wa kowane mutum daya da kyautar naira 50,000 da yadin shadda 10. Mu na yi masa addu'ar Allah ya saka masa da alheri."
Tuni dai wadannan mutane suka kama hanyar komawa cikin iyalin su, tare da bayyana matikar farinciki da godiya ga shugaban Majisar Dattawan, kana da addu'ar Allah ya cika masa burinsa bisa ga faranta musu da yayi a daidai wannan lokaci na watan Ramadan mai tsarki.
managarciya