Shugaban Kwastam Ya Jagoranci Garƙame Dukkanin Iyakokin Najeriya Da Nijar

Shugaban Kwastam Ya Jagoranci Garƙame Dukkanin Iyakokin Najeriya Da Nijar

Muƙaddashin shugaban hukumar hana fasa ƙwauri ta Nijeriya, Bashir Adewale Adebola ya ziyarci jihar Katsina tare da tabbatar da umurnin shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu na rufe iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

Adewale ya ziyarci iyakar Najeriya da Nijar ta Magama Jibiya tare da wasu daga cikin manyan shuwagabannin hukumar da suka yi Mashi rakiya.

Shugaban hukumar Bashir Adewale ya ce ya zo jihar ne domin cika duk wani umurnin da shugaban ƙasar Tinubu ya bayar kasancewar sa shugaban ECOWAS.

Ya ce "Da zarar abubuwa suka tafi yadda ake so yana da tabbacin za a sake buɗe iyakokin."

A lokacin ziyarar, Mukaddashin Shugaban hukumar ya kuma yi taro da mazauna yankunan wurin tare da sanar da su cewa, an ɗauki matakin ne domin fahimtar da masu juyin mulkin Nijar kan rashin dacewar abinda suka yi gami da maida zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mouhammad Bazoum.

A cewar sa, da zaran an samu nasarar da ake son samu, za'a buɗe iyakokin domin ci gaba da harkokin su na yau da kullum, gami da ci gaba da kasuwancin su.

Ya yi kira a gare su da su baiwa gwamnati haɗin kai kan ƙoƙarin ta na maido da mulkin dimokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar.

A jawabansu daban-daban, mazauna yankin sun tabbatar da baiwa ECOWAS haɗin kai domin ganin an samu nasarar da ake son samu a Nijar.