Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara Ahmad Sani Ya Rasu

Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara Ahmad Sani Ya Rasu

 

 

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara, Ahmad Sani Kaura ya riga mu gidan gaskiya, Channels Tv ta ruwaito. An ruwaito cewa, ya yanki jiki ya fadi ne a ranar Laraba a Gusau yayin wani taron zaman lafiya da aka gudanar da majalisar Ulama kan zaben 2023 mai zuwa. 

Jigon na PDP a jihar, Aminu Umar ya bayyana cewa, Kaura ya kasance ba shi da lafiya, kuma bai murmure ba lokacin da ya halarci wannan zama. 
Rasuwarsa na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da aka zabe shi ya zama shugaban PDP a jihar ta Zamfara, Sahara Reporters ta ruwaito.