Joash ya nemi jam’iyyar ta dauki darasi ga rikicin jam’iyyun da ya faru a jihohin Zamfara da Filato, wanda ya sabbaba soke nasarar wasu ‘yan takarar gwamnoninsu.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, Amupitan ya ce ci gaba da gudanar da tarukan na ADC na iya haifar da mummunan sakamako na fuskantar fushin doka.






