Shugaban hukumar tattara bayanan sirri ya ajiye aiki bayan ganawa da Tinubu 

Shugaban hukumar tattara bayanan sirri ya ajiye aiki bayan ganawa da Tinubu 

 

Shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya, Ahmed Rufai Abubakar ya sanar da ajiye muƙaminsa.

 
Yayin da ya ke jawabi ga maneman a fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu, Ahmed Rufai ya gode wa shugaban ƙasar bisa ba shi damar ci gaba da jagorantar hukumar bayan da ya zama shugaban ƙasa.
 
BBC Hausa ta rawaito cewa Ahmed Rufai ya ce ya je fadar shugaban ƙasar domin ganawa da shi, da yi masa bayanai kamar yadda ya saba a koyaushe, bayan nan ne kuma ya miƙa masa takardar ajiye aikinsa.
 
“Bayan na yi masa jawabi, na kuma gabatar masa da takardar ajiye aikina, kuma shugaban ƙasar ya karɓeta tare da amincewa da ita'', kamar yadda ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasar.
 
To sai dai bai yi cikakken bayani kan dalilinsa na ajiye aikin a daidai wannan lokacin ba.
 
Ya kuma ce yana alfahari bisa aikin da ya yi da shugabannin ƙasar har guda biyu.
 
A watan Janairun 2018 ne dai tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar, bayan korar tsohon shugaban hukumar Ayo Oke, bisa zargin rashawa.
 
Saukar shugaban na NIA na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da ƙamari a Najeriya, musamman yankunan arewacin ƙasar, inda 'yan bindiga ke zafafa hare-hare, tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.