Shugaban Hukumar malanta ta kasa, Farfesa Maitafsir ya soma aiki
Shi ne ke da kwalegin Ilimi ta Biga maizaman kanta da ke baiwa matasan da basu da galihu gurabun karatu, a kwalejin daga jihohin Sokoto,Kebbi,da Zamfara.
Shugaban Hukumar malanta ta kasa, Farfesa Maitafsir ya soma aiki
Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal Sokoto.
Maigirma Shugaban kasa Muhammad Buhari ya aminta da nadin Sabon Shugaban kula da ma'aikatar Malanta ta kasa, waton babban daraktan hukumar Farfesa Musa Garba Maitafsir wanda tuni ya isa sabon ofishin sa kuma ya fara aiki, inda ya samu tarbon manyan ma'aikatan hukumar, ya bada tabbacin barin kofar sa a bude domin cimma burin Maigirma Shugaban kasa, wajen inganta aikin sa.
Farfesa maitafsir, Wanda yake dan asalin karamar Hukumar Mulkin Yabo ne da ke jihar Sokoto tarayyar Nageriya Wanda ya taba rika hukumar ilmi ta bai daya,kuma yayi kwamishinan lamurran Addinin Musulunci duk a jihar Sokoto Wanda Kafin nadin yana aiki ajami'ar dan fodiyo da ke jihar Sokoto.
Shi ne ke da kwalegin Ilimi ta Biga maizaman kanta da ke baiwa matasan da basu da galihu gurabun karatu, a kwalejin daga jihohin Sokoto,Kebbi,da Zamfara.
managarciya