Shugaba Tinubu Yana nan bai ɓata ba — APC Ga Peter Obi
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Lagos ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai ɓace ba kuma bai yi watsi da aikinsa ba, duk da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.
APC ta mayar da martani ne kan kalaman Peter Obi, inda ta ce irin waɗannan maganganu ba su da tushe, kuma ana yin su ne don tayar da hankalin jama’a.
A cewar jam’iyyar, Tinubu na gudanar da harkokin ƙasa yadda doka ta tanada, ciki har da tarurruka da tattaunawa da manyan jami’an gwamnati, tare da bin tsare-tsaren da za su kawo ci gaba ga ƙasar nan.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su guji yada bayanai marasa tushe, tare da jan hankali cewa Najeriya na buƙatar haɗin kai da fahimta, ba jita-jita ba.
APC ta jaddada cewa Shugaban Ƙasa na nan daram, yana bakin aiki — duk wani labarin ɓacewarsa ƙarya ce tsagwaron-ta!






