Shugaba Buhari zai tafi ƙasar Habasha a ranar Litinin
Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Habasha waton Ethopia domin halartar taron rantsar da Firai Ministan kasar Abiy Ahmed a wa'adinsa na biyu da za a yi a yi a ranar Litinin a birnin Addis Ababa.
Shugaba Buhari zai tafi ƙasar Habasha a ranar Lahadi
Daga : Janaidu Amadu Doro.
Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Habasha waton Ethopia domin halartar taron rantsar da Firai Ministan kasar Abiy Ahmed a wa'adinsa na biyu da za a yi a yi a ranar Litinin a birnin Addis Ababa.
Shugaba Buhari dai zai bar birnin Abuja a gobe Lahadi zuwa babban birnin Habasha kuma zai gabatar da jawabin fatan alheri a taron rantsuwar.
Ana sa ran kuma daga nan zai halarci liyafar cin abinci tare da sauran shuwagabannin ƙasashe.
Daga cikin wadanda za su mara wa Shugaban kasar baya a tafiyar akwai : ministan harkokin ƙasashen waje Geoffery Onyeama da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta NIA Ambasada Ahmed Rufai Abubakar da sauransu.
Bayan kammala bukukuwan rantsuwar shugaban zai dawo gida Najeriya a ranar Talata mai zuwa.
Allah ya sa a je lafiya Kuma a dawo lafiya.
managarciya