Shugaba Buhari Ya Sake Gargaɗin 'Yan Bindiga
Buhari ya yi wannan furucin ne tun daga South Africa, yayin da yake Allah wadai da kisan mutum 15 da yan bindiga suka yi a Goronyo da Illela, jihar Sokoto. Babban mai taimakawa shugaban kasa ta bangaren yada labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar mai taken, "Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutum 15 a Sokoto." Buhari yace: "Wannan rashin imanin da ake wa mutanen da basu ji ba ka ba su gani ba ya isa haka, ba zamu barshi ya tafi salin alin ba."
Shugaba Buhari Ya Sake Gargaɗin 'Yan Bindiga
Daga Comr Abba Sani Pantami
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gargadi 'yan bindiga kada su yi tunanin banza suke ci, ba za'a kawar da su ba.
Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa ba zata bari 'yan Najeriya su cigaba da fama da kalubale kala daban-daban daga 'yan bindigan ba.
Buhari ya yi wannan furucin ne tun daga South Africa, yayin da yake Allah wadai da kisan mutum 15 da yan bindiga suka yi a Goronyo da Illela, jihar Sokoto.
Babban mai taimakawa shugaban kasa ta bangaren yada labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar mai taken, "Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutum 15 a Sokoto."
Buhari yace: "Wannan rashin imanin da ake wa mutanen da basu ji ba ka ba su gani ba ya isa haka, ba zamu barshi ya tafi salin alin ba."
"Ina mai kara tabbatarwa 'yan Najeriya cewa gwamnatin mu ba zata barsu haka nan ba, su cigaba da fama da matsalolin 'yan bindigan daji."
managarciya