Shirin rage raɗaɗi ba zai yi maganin talauci ba a Najeriya – Masana
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
'Yan Najeriya har yanzu suna fama da matsin rayuwa a lokacin da suke kokarin neman abin rufin asiri, yayin da suke fuskantar tsadar kayan abinci da hauhawar farashi.
Hakan na zuwa ne wata biyar bayan gwamnatin kasar ta fitar da kuɗi har naira biliyan 72 domin shirin rage raɗaɗi, sakamakon matsin rayuwar da aka shiga bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun bara.
Wani kwararre kan al'amuran ci gaban duniya, Dr Hussaini Abdu ya yi wa BBC bayani kan dalilin da ya sa shirin rage radadin bai cimma buri ba.
A cewar sa tallafi ba ya magani kai tsaye musamman kan abin da ya shafi tattalin arziki saboda "ana yi ne domin a cikin takaitaccen lokaci a rage nauyi, kafin ka farfado ka nemi abin yi."
Kwararren ya ce mafi yawan al'umma sun ce an raba kayan tallafi amma ba su gani a kasa ba dalilin da ya sa ya ce ya kamata a ce an dauki lokaci ana aiwatar da tsarin tare da ware adadin da za a rika bai wa mutane.
Dr Abdu ya soki tsarin da aka bi wajen yin rabon kayan tallafin da ya ce irin tsarin ba ya "taɓa maganin talauci a ko ina."
"Abu ne aka yi ba kan tsari ba, saboda haka ba yadda za a yi a ce ya yi maganin irin wannan abun." in ji Dr Abdu.
Ya kara da cewa har yanzu akwai jihohin da ko "ƙwandala" ba su gani ba duk da iƙirarin gwamnati cewa ta fitar da kuɗaɗe ga jihohi domin rage raɗaɗin da al'umominsu ke fuskanta.
managarciya Oct 30, 2021 12 169
managarciya Feb 3, 2025 3 110
Maryamah Dec 14, 2021 2 88
Maryamah Dec 16, 2021 10 74
managarciya Jun 24, 2023 5 73
managarciya Nov 13, 2023 0 550
managarciya Nov 12, 2023 0 346
managarciya Nov 12, 2023 0 335
managarciya Nov 12, 2023 0 416
managarciya Nov 11, 2023 1 702
managarciya Oct 30, 2021 0 330
Haka kuma idan an samu juna biyu, matan karkara awo ba dole ba ne a wurin mazajen...
managarciya Jan 1, 2025 0 207
managarciya Jan 1, 2024 0 299
Wasu mutane na ganin tun farko gwamnti ta yi ragon azanci don bai kamata ta sayi...
managarciya Apr 3, 2023 0 359
managarciya Jun 14, 2024 0 450
Saɓanin abinda ke tafiya a yanzu, a lokacin gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal, sai...