Shekara 36 na kwashe a harkar Finafinnan Hausa------Hajara Usman

Managarciya na hasashen girma da mutunci da kimar da ta riƙe na tsawon shekarru ga idon makallata wasan Hausa na Kannywood da wuya bai sauka ba a lokacin da za su kalli wani sabon shiri da ake kan ɗauka a yanzu GWARAMA da ta fito a matsayin matar wanda ta girma, abin da ake kira Suger Mommy.

Shekara 36 na kwashe a harkar Finafinnan Hausa------Hajara Usman
Shekara 36 na kwashe a harkar Finafinnan Hausa------Hajara Usman

Shekarata 36 Na Kwashe A Harkar Fina-finan Kannywood, Cewar Jaruma, Hajara Usman a wata hira da aka yi da ita.

Ni 'yar Asalin Jihar Gombe Ce, Amma A Lagos Na Tashi. Zuwa Yanzu Na Dauki Shekaru Akalla Talatin Da Shidda Ina Fito Wa A Cikin Fina-finnai.

Mafi yawancin Jaruman Masana'antar Fina-finai Maza Da Mata na Taɓa Fitowa A Matsayin Mahaifiyarsu A Cikin Fim. Na Taɓa Aure Har Sau Biyu, Ina Da Yara Uku.

Halin yanzu kusan ita kaɗai ce tsohuwa mafi daɗewa a harkar finafinnan Hausa, duk wasu na ganin kamar Rabi Sufi na iya shiga gabanta a wurin fara harkar finafinnan.

Kafin wannan hirar wasu sun ɗauka Hajara Usman 'yar asalin Kano ce ganin yanda ta samu karɓuwa a hsrkar wasan a tsakanin masu shiryawa da ba da umarni a wasan kwaikwayo na Hausa.

Hajara Usman ta ƙware a harkar shirya finafinnai takan kuma riƙe mutuncinta ba ta fitowa a rawar da mutanen gari za su zage ta ko su aibanta abin da ta yi wasar da aka yi.