Shekara 2: Sanata Lamiɗo ne yafi samarwa matasa aikin yi
Ɗan majalisar dattijai mai wailtar Sakkwato ta Gabas Sanata Ibrahim Lamiɗo ya soma bukin cikar shekara biyu, yana wakiltar yankinsa a zauren Majalisa, ya fara da miƙa takardar soma aiki ga wasu matasa 10 da suka fito a kananan hukumomi takwas da yake wakilta a ranar Jumu'ar nan.
Sanata ya samo gurbin aiki a hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa, aikin yanada matukar muhimmanci ga cigaban yankinsa da jihar Sakkwato baki daya.
Sanata Lamido zai kaddamar da muhimman aiyukkan raya ynkin da al'umma a kwanannan don ganin ya fitar da mutanen sa a cikin kishirwar rashin ababen more rayuwa, kari da wadanda ya yi a shekarar data gabata.
A tun sanda Sanata Lamido ya soma aikin wakiltar yankin Sakkwaato ta Gabas bai tsaya ba domin ganin an samar da tsaro a yankin, ya kuma ga harkar ilmi ta bunkasa hakan ya sanya shi tura dimbin matasa kasar Indiya don yin karatun digiri na daya dana biyu, ga kuma shirin da yake da shi na tura mata matasa zuwa kasar Saudiya don yin karatun likitanci.
A shekara biyu ta Sanata Lamido kwaliya ta biya kudin sabulu ganin yanda yake wakilci da tunanin jama'arsa da kokarin samar da abubuwan dogaro ga mutanensa domin shi ya aminta mutane su zama masu dogaro da kansu, sabanin wasu da ke son mutane su zamaa bayinsu, suna yin maula a tsakaninsu don samun abin kaiwa a baki.
managarciya